logo

HAUSA

Ministan Harkokin Kasuwanci na Sin Wang Wentao Ya Gana Da Darakta Janar Ta WTO Ngozi Okonjo-Iweala

2023-05-27 16:29:37 CMG Hausa

Ministan kula da harkokin kasuwanci na kasar Sin Wang Wentao, ya gana da Darakta Janar ta kungiyar cinikayya ta duniya WTO Ngozi Okonjo-Iweala, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayi kan wasu batutuwan da suka shafi shirye-shiryen taron ministocin harkokin kasuwanci na kasashen WTO karo na 13 ( MC13) da sauransu.

Wang Wentao ya gana ne da Ngozi Iweala a jiya Jumma’a, yayin da yake halartar taron ministocin kasuwanci na kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin Asiya da tekun Pasific (APEC) a birnin Detroit na kasar Amurka.

A yayin ganawar, Okonjo-Iweala ta yaba da kyakkyawar rawar da kasar Sin take takawa a cikin kungiyar WTO, inda ta bayyana fatan ganin kasar Sin ta ci gaba da ba da jagoranci wajen cimma nasara a yayin taron MC13.

A nasa bangaren, Wang Wentao ya bayyana cewa, kasarsa tana aiwatar da ainihin ra’ayin kasancewar bangarori da dama, kana tana taka rawar gani wajen yin gyare-gyare a WTO, kuma za ta gudanar da ayyuka masu amfani da za su bayar da gudummawa ga cimma nasarar taron MC13.

A yayin taron dandalin, Wang Wentao ya kuma gana da wakiliyar kasuwanci ta kasar Amurka Katherine Tai, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayi sosai bisa gaskiya kuma a zahiri, kan dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Amurka da Sin, da kuma batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na bangarori da dama da ke jan hankulansu duka. (Mai fassara: Bilkisu Xin)