logo

HAUSA

Neman ganin ci gaban kimiyya da fasaha ya amfani jama’ar kasashe daban daban

2023-05-26 16:33:45 CMG HAUSA

A kwanan nan ana gudanar da taron dandalin kimiyya da fasaha na ZGC a birnin Beijing na kasar Sin, inda shugaba Xi Jinping na kasar ya aika da sakon taya murnar kaddamarwar taron.

Cikin sakonsa, shugaban ya ce, a yanzu haka, ana kokarin gudanar da sabon zagayen juyin juya hali kan kimiyya da fasaha, da inganta tsare-tsaren masana’antu. Sai dai don neman samun ci gaban al’ummu daban daban na bai daya, ana bukatar hadin gwiwar mabambantan kasashe, da matakin bude kofa da more ci gaban da aka samu tare, fiye da yadda ake da wannan bukata a baya. Ya ce kasar Sin a nata bangare, tana tsayawa kan manufar bude kofa, da amfanawa juna, da cin moriya tare, inda take son hada gwiwa da sauran sassan duniya a kokarin kirkiro sabbin fasahohi, da neman ganin ci gaban kimiyya da fasaha ya amfani jama’ar kasashe daban daban.