logo

HAUSA

Sin ta bukaci a tallafawa AU kan aikin wanzar da zaman lafiya

2023-05-26 15:23:09 CMG Hausa

Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya, ya furta a jiya Alhamis cewa, ya kamata gamayyar kasa da kasa su yi kokarin samar da tallafi ga kungiyar kasashen Afrika ta AU, kan aikin da take yi na wanzar da zaman lafiya, kana kasar Sin na fatan ganin kwamitin sulhun MDD ya ba da taimako a fannin, ta yadda za a iya daidaita al’amura cikin sauri.

A cewar jami’in na kasar Sin, don samarwa kungiyar AU da kudin da take bukata a fannin aikin wanzar da zaman lafiya, ya kamata a tsaya kan manufar daidaita batutuwan nahiyar Afirka ta dabarun iri na nahiyar Afrika. Wato bayan kungiyar AU ta karbi tallafin da MDD ta samar, aikin kungiyar na wanzar da zaman lafiya zai ci gaba da zama karkashin kulawarta. Yana mai cewa, matsalar kudi kawai za a daidaita, maimakon sanya rundunar kungiyar AU ta zama wata runduna ta daban ta MDD.

Zhang ya kara da cewa, kasar Sin tana tsayawa kan kokarin rufawa nahiyar Afirka baya, ta yadda za ta samu karin karfin kiyaye zaman lafiya. Kana kasar na son ganin kungiyar AU ta samu isashen tallafi, wanda zai dore, kuma ake iya hasashen adadin da za a samu, don aiwatar da aikin kare zaman lafiya bisa karfin kanta. Haka kuma kasar Sin na fatan ganin kwamitin sulhun MDD ya yi amfani da damar da taro na wannan karo ya samar, wajen neman samun takamaiman ci gaba a yunkurin daidaita al’amarin. (Bello Wang)