logo

HAUSA

Sakatare Janar na MDD ya bukaci kasashen duniya su goyawa nahiyar Afrika baya

2023-05-26 11:38:43 CMG HAUSA

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya bukaci kasashen duniya su goyi bayan nahiyar Afrika, inda ya yi kira da samarwa nahiyar wakilcin da ya dace a tsarin hada-hadar kudi na duniya.

A cewarsa, kuzarin nahiyar Afrika abu ne da ba za a iya dakatarwa ba, haka kuma tana da dimbin damarmaki, sai dai, rashin adalci a fannin tattalin arziki na tarnaki ga ci gabanta.

Antonio Guterres ya bayyana haka ne a sakonsa domin ranar Afrika ta duniya dake gudana ranar 25 ga watan Mayun kowacce shekara domin jinjinawa nasarorin da Tarayyar Afrika (AU) ta samu tun bayan kafuwarta a ranar 25 ga watan Mayun 1963.

A cewarsa, kasashen Afrika ba sa samun wakilcin da ya kamata a hukumomin tafiyar da harkokin duniya, daga Kwamitin Sulhu na MDD zuwa tsarin musayar kudaden ketare na Bretton Woods, haka kuma ana hana su samun rangwamen biyan bashi da ma basussukan da suke bukata.

Har ila yau, ya ce ya kamata bankunan raya kasa da kasa su sauya tsarinsu na kasuwanci da samar da kudade domin jan hankalin bangarori masu zaman kansu kan farashi mai rahusa ga kasashe masu tasowa. Ya kara da cewa, ya kamata kasashe masu tasowa su samar da tallafin da suka yi alkawarin samarwa ga ayyukan tinkarar sauyin yanayi da sauransu. (Fa’iza)