logo

HAUSA

Ma'aikatar Kasuwancin Sin: Ministan kasuwancin Sin zai gana da takwararsa na Amurka

2023-05-25 19:36:55 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Shu Jueting, ta bayyana cewa, daga ranar 25 zuwa 26 ga watan nan, ministan kasuwanci na kasar Sin Wang Wentao, zai halarci taron ministocin cinikayya na kungiyar APEC, inda zai yi shawarwari tare da sakatariyar harkokin kasuwancin Amurka Gina Raimondo, da kuma wakiliyar kasuwanci Catherine Tai, domin yin musayar ra’ayoyi kan dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, da kuma wasu batutuwan da suke jawo hankulan bangarorin biyu.

Shu ta bayyana hakan ne a yayin taron manema labaru da aka saba yi, a yau Alhamis 25 ga wata.

Dangane da tambayar kafofin watsa labaru, game da ko za a iya samar da sauyi game da cinikin sassan na’urorin laturoni ko a’a, sakamakon dakatar da sayayya daga kamfanin Micron na Amurka da ofishin nazarin harkokin tsaron yanar gizo na kasar Sin ya yi, Shu ta bayyana cewa, hukumar da abun ya shafa ta kasar Sin, ta riga ta fitar da bayanai kan yadda ake bitar kayayyakin Micron da ake sayarwa a kasar Sin. Kuma binciken wani mataki ne da ya wajaba, don kare tsaron kasar Sin.

(Mai fassara: Bilkisu Xin)