logo

HAUSA

Xi Jinping ya amsa wasikar malamai da dalibai na jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Macau domin karfafa musu gwiwa

2023-05-25 16:25:08 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar wakilan malamai da dalibai na jami'ar kimiyya da fasaha ta Macau, wadanda suka shiga aikin samar da tauraron dan Adam mai suna "Macau Science-1", don ba su kwarin gwiwa. 

A wasikarsa ta ranar 23 ga wata, Xi Jinping ya ce, “daga cikin abubuwan da kuka bayyana, na yi sha'awar aikinku da nauyin da ya rataya a wuyanku na sadaukar da kai ga harkokin kimiyya da fasaha na kasar, da gina kasa mai karfi a fannin fasahohi masu alaka da sararin samaniya. Na yi farin cikin jin cewa an harba tauraron dan Adam na "Macau Science-1" da kuka taka rawa wajen tsara shi cikin nasara, kuma ina son taya muku murna. ”(Safiyah Ma)