logo

HAUSA

Layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti ya fara jigilar motar daukar kaya

2023-05-25 10:38:52 CMG Hausa

Layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti da kasar Sin ta gina, ya fara jigilar motocin daukar kaya a jiya Laraba, daga tashoshin ruwan Djibouti, zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha.

Kashin farko na motocin 63 sun isa tashar Indode dake wajen birnin Addis Ababa a jiya Laraba, inda aka gudanar da wani biki na musammam a tashar domin isarsu.

Ministan kula da sufuri da jigila na Habasha Denge Boru, ya bayyana lamarin a matsayin muhimmin ci gaba ga yunkurin Habasha na inganta bangaren sufuri da jigila.

Da yake bayyana isar motocin a kwana guda kacal kuma cikin inganci da tsimin lokaci da albarkatu, ministan ya jaddada karin gudunmuwar da layin dogon ke bayarwa wajen inganta cinikin shige da ficen kayayyaki a kasar ta gabashin Afrika. (Fa’iza Mustapha)