logo

HAUSA

Layin dogo na Habasha zuwa Djibouti na kara habaka hada hadar sufuri a yankin kahon Afirka

2023-05-25 16:50:17 CMG Hausa

Layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti da kasar Sin ta gina, ya fara jigilar motocin daukar kaya a jiya Laraba, daga tashoshin ruwan Djibouti, zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha.

Kashin farko na motocin 63 sun isa tashar Indode dake wajen birnin Addis Ababa a jiya Laraba, kuma ministan kula da sufuri da jigila na Habasha Denge Boru, ya bayyana lamarin a matsayin muhimmin ci gaba ga yunkurin Habasha na inganta bangaren sufuri da jigila.

A hakika, tun bayan kaddamar da layin dogo na sufurin hajoji da jama’a, wanda ya hada kasar Habasha maras iyaka da teku da kasar Djibouti a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2018, yau sama da shekaru biyar, layin dogon na ta kara samun tagomashi, ta fannin bunkasa hada hadar sufuri, da kasuwanci tsakanin kasashen biyu, da ma kasashen dake shiyyar ta kahon Afirka.

Karkashin wannan katafaren aiki na ginin layin dogo da kasar Sin ya kammala tun a shekarar 2017, yanzu haka kasar Habasha ta samu babbar damar shigarwa, da fitar da manyan hajoji ta tashoshin jiragen ruwan na Djibouti. Har ma wasu alkaluma sun shaida yadda kaso sama da 95 bisa dari, na hajojin cinikayyar kasar Habasha ke bi ta tashoshin ruwan Djibouti.

Ko shakka babu wannan babban ci gaba ne a tarihin yankin kahon Afirka.

Muna iya gani daga sakamakon ci gaban da layin dogon ya haifar, cewa baya ga saukaka safarar hajoji, jiragen kasa dake bin layin dogon, sun kuma saukaka sufurin fasinjoji, ta hanyar rage farashin zirga zirga tsakanin sassan kasashen biyu.

Irin wadannan nasarori da layin dogon ke samu, sun tabbatar da burin da kasar Sin tare da abokan huldar ta na nahiyar Afirka ke fatan cimmawa, ta fuskar gudanar da hadin gwiwa mai dorewa, wanda ke ingiza ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummun kasashe masu tasowa.

Ko shakka ba bu layin dogo na Habasha zuwa Djibouti, na ci gaba da bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu, da ma sauran kasashen yankin kahon Afirka, ta fuskar saukaka farashi, da lokacin safarar hajoji, baya ga kara inganta yanayin sufuri, da samar da karin guraben ayyukan yi ga al’ummun kasashen yankin, matakin da masharhanta ke ganin zai ci gaba da fadada cinikayya, da hada hadar shige da fice tsakanin kasashen yankin gabashin Afirka baki daya. (Saminu Alhassan)