logo

HAUSA

Najeriya ta ce dalar biliyan 8 ta kashe kafin an kawo karshen yakin basasar kasar Liberia

2023-05-25 09:52:50 CMG Hausa

Babban hafsan tsaron Najeriya Leo Irabor ya tabbatar da cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya ta kashe tsabar kudi har dalar biliyan 8 wajen kawo karshen yakin basasar kasar Liberia wanda ya faru a tsakanin 1989 zuwa 1997 da kuma wanda ya faru a tsakanin 1999 zuwa 2003.

Babban hafsan tsaron na Najeriyar ya bayyana hakan ne jiya Laraba 24 ga wata a birnin Abuja yayin da yake gabatar da jawabi a wajen biki karo na 75 na tunawa da aikin wanzar da zaman lafiya na dakarun majalissar dinkin duniya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

General Leo Irabor ya ce baya ga asarar rayukan dakarun ta da kuma raunika da wasu jami’an ta suka samu, Najeriya ta ci gaba da kashe kudade har zuwa karshen yakin, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 200,000 yayin da miliyoyi kuma suka kauracewa muhallan su.

Ya ce a wancan lokaci dakarun Najeriyar sun yi aiki ne karkashin kungiyar kasashen ECOWAS mai wakilan kasashe 16 da suka samar da dakarun tsaron hadin gwiwa na ECOMOG, wanda kuma ta kasance bisa jagorancin dakarun Najeriya.

Babban hafsan tsaron na Najeriya ya ce, Najeriya ta bayar da gudummowar aikin wanzar da zaman lafiya har sau 41 a sassa daban daban na duniya, inda ya kara da cewa, sama da dakarun Najeriya 200,000 ne suka yi aiki kai tsaye karkashin shirin wanzar da zaman lafiya na majalissar dinkin duniya, kuma wasu daga cikin manyan jami’an sojin kasar sun jagoranci da yawa daga cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya da majalissar ta shiga.

Haka kuma karkashin shirin hadin gwiwa a tsakanin kasashen dake nahiyar Afrika, Najeriya ta shiga aikin wanzar da zama lafiya a kasashen Cote d’Ivoire, Guinea-Bissau, Gambia, Liberia, Mali, Darfur da Saliyo, inda ta bayar da gudummowar kudade, kayan aiki, sojoji da kwararru fararen hula a fagen wanzar da zaman lafiya.

A nasa jawabin sa, babban bako na musamman a wajen bikin, tsohon babban hafsan Sojin Najeriya Martin Luther Agwai cewa ya yi, shirin wanzar da zaman lafiya na majalissar dinkin duniya wani mahimmin mataki ne da yake taimakawa kasashen wajen kawo karshen duk wasu  rikice-rikice.

Ya ce tun daga 1948 adadin dakarun soji da jami’an tsaron farin kaya sama da miliyan 2 ne suka bayar da gudummowa wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaba a kasashen daban daban na duniya.(Garba Abdullahi Bagwai)