logo

HAUSA

Guterres: Yankin ciniki cikin ‘yanci na Afrika zai ingiza ci gaba mai dorewa

2023-05-25 10:06:21 CMG Hausa

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya bayyana irin muhimmiyar rawar da yankin ciniki cikin ‘yanci na Afrika zai taka wajen tabbatar da ci gaba mai dorewa a nahiyar.

A cewarsa, bisa ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD da ake son cimmawa zuwa 2030 da ma ajandar AU ta 2063, dole ne a zage damtse a kokarin da ake na yin cikakken amfani da damarmakin cinikayya da masana’antu, wajen inganta ci gaba mai dorewa a kowanne bangare.

Antonio Guterres ya bayyana haka ne a rana ta karshe ta taron tattauna batutuwan Afrika ta shekara-shekara da aka yi a birnin New York na Amurka, inda a bana aka mayar da hankali kan gaggauta aiwatar da yarjejeniyar yankin ciniki cikin ‘yanci ta Afrika, dake zaman irinta mafi girma a duniya.

A cewarsa, burin shi ne yankin ya kasance wani jigo na samun ci gaba. Ya kara da cewa an rasa galibin ci gaban da kasashen Afrika da dama suka samu kafin bullar COVID-19, bayan bullar annobar, yana mai bayyana bukatar kara kokarin tabbatar da samun kasuwar bai daya ta nahiyar.

Bugu da kari, ya ce kiyasi na baya-bayan nan ya nuna cewa, aiwatar da dukkan yarjejeniyar kafa yankin ke iya samar da karin kudin shiga da zai kai kaso 9 a shekarar 2035. Yana mai cewa adadin zai iya fitar da mutane miliyan 50 daga kangin talauci da rage rashin daidaiton kudin shiga. (Fa’iza Mustapha)