logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su yi kokarin tabbatar da wadatar abinci

2023-05-24 14:02:22 CMG Hausa

Zanaunnen wakilin kasar Sin dake MDD, Zhang Jun, ya yi kira ga kasashen duniya a jiya Talata da su warware rikici cikin lumana ta hanyar tattaunawa, don taimakawa yankuna dake fama da rikici cimma zaman lafiya da kwanciyar hankali cikin sauri, da samar da yanayi mai kyau don kare tsaron fararen hula tare da tabbatar da wadatar abinci.

A yayin bude muhawarar kwamitin sulhu kan batun samar da abinci da kare fararen hula daga hargitsi da aka gudanar jiya, Zhang Jun ya yi kira ga bangarorin dake gwabzawa da juna da su mutunta kudurin kwamitin sulhu mai lambar 2417 da ta 2573, domin kare tsaron fararen hula bisa dokar jin kai da sauran dokokin kasa da kasa, musamman ma mata da kananan yara, da kuma tabbatar da agajin jin kai ba tare da cikas ba. Kana ya dace kasa da kasa su gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninsu a maimakon nuna kiyayya ga juna bisa ka'idoji MDD, ta yadda za a samar da yanayi mai kyau yayin kokarin shimfida zaman lafiya. 

Zhang Jun ya kara da cewa, kasar Sin tana yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya a ko da yaushe domin samar da isasshen abinci ga al’ummomin kasa da kasa, kuma tana son ci gaba da yin kokari tare da su domin aiwatar da shawarar raya duk duniya da ta gabatar, da zurfafa hadin gwiwa a fannin samar da abinci da rage talauci, da gina duniya tare da kawar da yaki da rikici da yunwa da kuma talauci.(Safiyah Ma)