logo

HAUSA

Kasar Sin ta kaddamar da bincike kan wasu jiragen ruwa guda biyu da suka nutse a cikin tekun kudancin kasar Sin

2023-05-24 11:10:35 CMG Hausa

Assalamu alaikum, masu kallonmu. Masu binciken tsofaffin kayayyakin tarihi na kasar Sin, sun kaddamar da bincike kan wasu jiragen ruwa guda biyu da suka nutse a cikin tekun kudancin kasar Sin shekaru aru-aru da suka gabata. Masanan sun kaddamar da binciken nasu ne a ranar Asabar din karshen makon jiya, wanda hakan ya bude wani sabon babi a ayyukan binciken kayayyakin tarihi da ake ganowa a karkashin teku mai zurfi.