logo

HAUSA

Tabbas za’a karyata jita-jitar dake shafawa jihar Tibet bakin fenti

2023-05-24 20:21:51 CMG Hausa

Jihar Tibet ta kasar Sin ta samu ‘yanci cikin lumana, a ranar 23 ga watan Mayun shekara ta 1951, al’amarin da ya tona asirin wasu gungun mutanen kasashen waje, na balle jihar daga cikin kasar Sin. Kana tun daga ranar, Tibet ta shiga sabon tarihi, inda miliyoyin bayi manoma suka samu ‘yancin kai, da cikakken tabbacin kare hakkin dan Adam da zama ginshikan kasa, ta hanyar yiwa jihar Tibet gyare-gyare bisa tafarkin demokuradiyya.

Wasu alkaluma sun shaida irin ci gaban da aikin tabbatar da kare hakkin dan Adam ya haifar a jihar, inda yawan GDPn jihar ta Tibet a shekarar 2022, ya karu har sau 346.8, idan aka kwatanta da na shekara ta 1951. Sa’annan matsakaicin yawan shekarun al’ummar jihar ya karu daga 35.5 a farkon lokacin da aka ‘yantar da jihar, har zuwa 72.19 a halin yanzu. Kana, kafin Tibet ta samu ‘yanci, yawan mutanen jihar da ba su taba shiga makaranta ba ya zarce kaso 95 bisa dari, amma yanzu, an kusan kawar da irin wannan matsala, har ma an kafa wani tsarin samar da ilimi ba tare da karbar kudi ba, na tsawon shekaru 15.

Tibet na kara samun ci gaba, amma akwai wasu ‘yan siyasar kasashen yammacin duniya, wadanda har yanzu suka yi biris da matukar kokarin da gwammatin kasar Sin ta yi na kyautata rayuwar al’ummar jihar, da rura wutar rikici kan batun da ya shafi hakkin dan Adam.

Babban dalilin da ya janyo ci gaban Tibet, shi ne ci gaban da duk kasar Sin ta samu. A halin yanzu, ana kokarin zamanantar da duk kasar, kuma Tibet tana nan cikin sabon mafari. Idan za’a iya hada ci gaban Tibet da ci gaban duk kasa tare, hakkin dan Adam a jihar zai kara tabbata, kana, al’ummar jihar za su kara jin dadin rayuwa. Babu tantama, za’a karyata jita-jitar dake yunkurin shafawa jihar Tibet bakin fenti. (Murtala Zhang)