logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Rasha

2023-05-24 19:32:15 CMG Hausa

Da maraicen yau Laraba 24 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da firaministan kasar Rasha, Mikhail Mishustin, wanda a yanzu haka yake ziyarar aiki kasar Sin.

Yayin zantawar ta su, Xi ya ce karfafawa, gami da raya dangantakar Sin da Rasha, babban fata ne na al’umma, kana abun da ake sa ran gani ke nan. Kana yana fatan bangarorin biyu za su yi kokari tare don ciyar da hadin-gwiwar su gaba zuwa sabon matsayi, da kara sanya sabbin abubuwa a cikin dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkanin fannoni, a sabon zamani tsakanin su.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar sa na fatan kara hada kai da Rasha, don ci gaba da marawa juna baya, a batutuwan da suka shafi babbar moriyar su, da fadada hadin-gwiwa a hukumomin dake kunshe da bangarori daban-daban, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar hadin-kan Shanghai wato SCO, da kungiyar BRICS, da kuma kungiyar kasashen G20 da sauran su.

A nasa bangaren, Mikhail Mishustin cewa ya yi, ziyarar aiki mai ma’anar tarihi, wadda shugaba Xi ya yi a Rasha a watan Maris din bana, babbar nasara ce. Kuma Rasha na fatan yin kokari tare da Sin don aiwatar da muhimman ra’ayoyi iri daya da shugabannin su suka cimma, da zurfafa hadin-gwiwar su daga bangarori daban-daban. Haka kuma, tana fatan kara hada kai tare da kasar Sin, don taimakawa kasancewar bangarori daban-daban a duniya, da inganta odar duniya, bisa tushen dokokin kasa da kasa. (Murtala Zhang)