logo

HAUSA

An yi bikin ba da lambar yabo ta tsarin gadon kayayyakin noma mai muhimmanci na 2023

2023-05-23 13:56:30 CMG Hausa

Hukumar kula da abinci da aikin gona ta MDD wato FAO a takaice, ta gudanar da bikin ba da takardar shaida ga tsarin gadon kayayyakin noma mai muhimmanci a duniya na shekarar 2023 a birnin Rome jiya Litinin, Wakilan sabbin wuraren tarihi guda 24 da aka amince da su a kasashe 12 na duniya sun halarci bikin, ciki har da wuraren tarihi na aikin gona guda hudu a kasar Sin,

Mataimakiyar direktan hukumar FAO Maria Helena Semedo ta godewa kasar Sin bisa gudummawar da take bayarwa wajen kiyaye kayayyakin noma da aka gada.

Hukumar FAO tana kiyaye tsarin halittu da noma da ilmi da al’adu bisa tsarin GIAHS. Ya zuwa yanzu, hukumar FAO ta gano tsare-tsare da wuraren tarihi guda 74 a cikin kasashe 24, ciki har da guda 19 a kasar Sin. (Zainab)