logo

HAUSA

Me ya sa Amurka take maimaita yunkurinta na marawa Taiwan baya wajen halartar babban taron kiwon lafiya na duniya a kowace shekara?

2023-05-23 22:11:39 CMG Hausa

Babu abun mamaki, an ki yarda da sanya wani shirin da wasu kasashe kalilan suka gabatar, na gayyatar Taiwan don ta zama ‘yar kallo, a jadawalin babban taron kiwon lafiya na duniya karo na 76. Kawo yanzu, Amurka ta riga ta sha kaye har sau 7 a jere, a irin wannan yunkuri na ta na marawa Taiwan baya, abun da ya shaida cewa, manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, babban fata ne na kowa da kowa, kana, yunkurin Amurka ba zai samu nasara ko amincewa ba a duniya.

Abun tambaya a nan shi ne, tun da ba ta taba yin nasara ba, me ya sa Amurka take maimaita marawa Taiwan baya? Manazarta na ganin cewa, wannan dabara ce da Amurka ta dade tana amfani da ita, wajen amfani da batun yankin Taiwan don kawo tsaiko ga kasar Sin, wato tana yunkurin maida batun Taiwan a matsayin wani batun da ya shafi kasa da kasa, da kirkiro “Sin daya Taiwan daya”, domin kalubalantar amincewar kasa da kasa.

Har wa yau kuma, mahukuntan yankin Taiwan su kan baiwa ‘yan siyasar Amurka kyautar dimbin kudade a kowace shekara, al’amarin da ya sa suke matukar fatan samun goyon-bayan Amurka. Don haka, a kowace shekara, idan lokaci ya zo, wasu ‘yan siyasar Amurka su kan bayyana goyon-bayan su ga Taiwan, don ta samu gurbin halartar babban taron kiwon lafiya na duniya, amma ba su damu da sakamakon ba. Saboda a wajen Amurka, yankin Taiwan wani abun wasa ne zalla, da take amfani da shi don neman cimma muradunta. (Murtala Zhang)