logo

HAUSA

Matsalar karancin gashin kai na addabar mutane

2023-05-23 11:29:26 CMG Hausa

 

A shekarun baya, karin matasa sun gamu da matsalar karancin gashin kai a kasar Sin. Masana sun bayyana cewa, akwai wasu dalilai da suka haddasa matsalar karancin gashin kai, duk da haka, zaman rayuwa ta hanyar da ta dace, ya fi amfanawa wajen kiyaye gashin kai.

To me ya sa matasa suka gamu da matsalar karancin gashin kai? Yin barci a makare, shan giya da taba fiye da kima, matukar son cin abinci mai yaji da man girke, rika rina gashi ko nannade gashi, da dai sauransu sun sanya karin matasa gamuwa da matsalar karancin gashin kai. Ban da haka kuma, akwai yiwuwar a gamu da matsalar ta karancin gashin kai sakamakon kwayoyin halitta na gado, rashin isasshen garkuwar jiki, babbar matsin lamba a tunanni, magani, rauni da wasu cututtukan musamman.

To, me za a yi idan an gamu da matsalar karancin gashin kai? Masana sun ba da shawarar cewa, zaman rayuwa ta hanyar da ta dace, yana da matukar muhimmanci wajen kauracewa matsalar karancin gashin kai.

Da farko wajibi ne a yi iyakacin kokarin tabbatar da yin barci isasshe, da kauracewa yin barci a makare. Na biyu kuma, kamata ya yi a kyautata tunani sosai, a kauracewa samun matsin lamba ko damuwa a tunani. Na uku kuwa, wajibi ne a yi iyakacin kokarin kauracewa yin amfani da matsefi na leda, wanda zai yi saukin samar da wani nau’in tarzomar wutar lantarki maras karfi, ta haka rairayi kan rufe gashin kai. Na hudu, kamata ya yi a ci abinci masu gina jiki, a kauracewa cin abinci mai yawan gishiri ko yaji ko man girke. Kana kuma ya fi kyau a kara cin hatsi, kayan lambu, ‘ya’yan itatuwa. Na biyar wato na karshe, kar a wanke gashin kai sau da dama fiye da yadda ake bukata. Ya fi kyau a wanke gashin kai a ko wadanne kwanaki 2 ko 3 cikin ruwa mai zafin digiri 40. Yayin da ake wanke gashin kai kuma, a tausa fatar kai a hankali a hankali. Bayan an gama wanke ganshin kan, ya fi kyau a busar gashin kan bisa karfin iska, a maimakon yin amfani da mabushin gashi da lantarki mai samar da iska mai matukar zafi.

Har ila yau kuma, madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin haske da cewa, idan an gamu da mummunar matsalar karancin gashin kai, tilas ne a je ganin likita cikin hanzari, in ba haka ba, yawan gashin kan zai kara raguwa, har ma ba za a iya samun sauki ba har abada. (Tasallah Yuan)