logo

HAUSA

China da Afirka sun zama tsintsiya madaurinki daya wajen gina al’ummomin su masu kyakkyawar makoma ta bai daya

2023-05-23 15:54:30 CMG Hausa

Sin kasa ce dake tasowa mafi girma a duniya, Afirka ma nahiya ce dake da yawan kasashe masu tasowa. Sin da Afirka suna da kamanceceniya a fannoni da dama, al’amarin da ya sa suka kara hada kansu.

A watan Maris din shekara ta 2013, ba jimawa da hawan sa ragamar mulkin kasar Sin, Xi Jinping ya ziyarci nahiyar Afirka, inda a karo na farko ya bayyana wa duk fadin duniya muhimman manufofin gwamnatin kasar sa kan nahiyar Afirka, wato “Sahihanci”, da “Sakamako na hakika”, da “Dangantakar abokantaka”, da kuma “Aminci”, da shaida cewa, Sin da Afirka za su kasance sahihan aminan arzikin juna har abada, da jaddada cewa har kullum, Sin da Afirka za su kasance al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. Ke nan tun daga wancan lokaci, an bude sabon babi a fannin raya zumunta tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

A cikin shekaru goman da suka gabata, a karkashin jagorancin shugabannin su, Sin da Afirka sun zurfafa hadin-gwiwa, da mu’amala a bangarorin da suka shafi tattalin arziki, da kasuwanci, da gina ababen more rayuwar al’umma da sauransu, al’amarin da ya kara samar da alfanu ga al’ummomin su baki daya.

A ranar 25 ga watan Maris din shekara ta 2013, a kasar Tanzaniya, shugaba Xi Jinping ya fara gabatar da jawabin sa da harshen Swahili, inda ya fara da cewa “Habari! Habari!”, wanda ke nufin “Barka! Barka!”. A cikin jawabin sa mai taken “Kasancewa aminan gaskiya da abokai na ainihi”, shugaba Xi ya bayyana cewa, ya kamata a nuna “sahihanci” a yayin da kasar Sin take raya hulda tare da kasashen Afirka, da neman samun “sakamako na hakika” wajen hadin-gwiwar bangarorin biyu. Sa’annan, idan ana son karfafa zumunta tsakanin Sin da Afirka, ya dace a raya “dangantakar abokantaka”. A karshe, idan ana son daidaita matsalolin da ka iya faruwa, dole a nuna “aminci”.

Ke nan, muhimman kalmomin hudu, wato “Sahihanci”, da “Sakamako na hakika”, da “dangantakar abokantaka”, gami da “aminci”, sun shaida manufofin gwamnatin kasar Sin kan kasashen Afirka, da kafa alkibla ga makomar hadin-gwiwar bangarorin biyu.

A cikin shekaru goman da suka gabata, sau hudu shugaba Xi Jinping yana ziyartar nahiyar Afirka, da halartar taron kolin dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka, ko kuma FOCAC a takaice a biranen Johannesburg da Beijing, gami da bikin bude taron ministoci karo na 8 na dandalin FOCAC tare da gabatar da jawabi, da bada shawarar gudanar da taron koli na musamman kan hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin dakile annobar numfashi ta COVID-19.

A wajen taron kolin dandalin FOCAC wanda aka yi a shekara ta 2015 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, shugaba Xi ya bayyana muhimmin ra’ayin sa a fannin inganta hadin-gwiwar Sin da Afirka a sabon zamanin da muke ciki, har ma shugaban kungiyar tarayyar Afirka wato AU a wancan lokaci, wanda kuma shi ne tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe ya bayyana cewa: “A lokacin baya, ‘yan mulkin mallaka sun kawo wa Afirka barna, amma yanzu kasar Sin tana kawowa kasashen Afirka sabuwar rayuwa.”

Daga baya yayin ziyarar aikin sa kasar Rwanda a shekara ta 2018, shugaba Xi ya zanta da takwaransa na kasar wato Paul Kagame, inda ya ce: “Yau da safe na tashi daga otel na zo fadar shugaban kasa cikin mota. Duk da cewa babu nisa, amma daga wasu kananan fannoni, zan iya kara fahimtar duk kasa. Akwai tsabtar titi a birnin Kigali, inda jama’a suka tarbe ni da hannu biyu-biyu, al’amarin da ya shaida cewa, shugaba Kagame ya kware wajen tafiyar da harkokin mulki.” Shi kuma Paul Kagame ya bayyana cewa: “Sin babbar kasa ce a duk duniya, Xi Jinping kuma babban jagora ne, amma yana nunawa Rwanda adalci, tare da goya mata baya wajen raya kasa, ko da yake ita karamar kasa ce wadda ta taba fuskantar manyan matsaloli a tarihi.”

Kwalliya ta biya kudin sabulu, wajen raya dangantakar kasar Sin da kasashen Afirka a cikin shekaru goman da suka gabata. A sabon zamanin da muke ciki, kasar Sin ta hada aikin raya kan ta, tare da kokarin samar da dauwamammen ci gaba ga kasashen Afirka, al’amarin da ya kara samar da alfanu ga al’ummomin bangarorin biyu.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka (AU) Moussa Faki Mahamat cewa ya yi, a yayin da ake gwagwarmayar kwato ‘yanci a Afirka, kasar Sin tana tare da ita. A yayin da take himmatuwa wajen halartar harkokin kasa da kasa, kasar Sin ma tana tare da ita.

A farkon watan Maris din shekarar da muke ciki, a karo na farko kasar Sin ta shigo da wani nau’in kayan marmari mai suna “Avacado” daga kasar Kenya, abun da ya baiwa al’ummar kasar Sin damar dandana wannan dan itace mai dadi daga Afirka. Daga ridi na kasar Tanzaniya, har zuwa gyada daga kasar Senegal, a ‘yan shekarun nan, ana kara samun ire-iren amfanin gona na kasashen Afirka, da suke shigowa kasuwannin China, wadanda ke samun karbuwa sosai. Wannan al’amarin ya nuna cewa, kasuwancin da ake yi tsakanin Sin da Afirka na bunkasa cikin sauri, musamman karkashin jagorancin muhimmiyar shawarar “ziri daya da hanya daya”.

A halin yanzu, kusan dukkan kasashen Afirka membobin dandalin FOCAC sun halarci ayyukan shawarar “ziri daya da hanya daya”, kuma kwalliya ta riga ta biya kudin sabulu.

A yankin kahon Afirka, layin dogon da ya hada Mombasa da Nairobi, gami da wanda ya hada Addis Ababa da Djibouti, sun taimaka sosai ga ci gaban tattalin arzikin yankin. A kasar Senegal dake yammacin nahiyar Afirka, ayyukan hako rijiyoyi sun daidaita matsalar karancin tsaftataccen ruwan sha da ta addabi mutane da yawa. A Afirka ta Kudu kuma, aikin samar da wutar lantarki bisa karfin iska ya taimaka sosai wajen yin tsimin makamashi, da rage fitar da iska mai gurbata muhalli. A Aljeriya dake arewacin Afirka, kasar Sin ta taimaka ta harba mata wani tauraron dan Adam na fannin sadarwa, domin samar da hidimar sadarwa ga al’ummar duk fadin kasar, musamman wadanda ke zaune a yankunan karkara, kuma irin wadannan al’amura na hadin-gwiwar Sin da Afirka domin cimma moriyar juna, ba sa misaltuwa.

Shugaba Xi Jinping ya taba bayyana cewa, babbar ma’anar raya huldodin Sin da Afirka ita ce, samar da ci gaba ga Afirka bisa ci gaban da kasar Sin ta samu, domin neman samun moriya tare. A duk fadin nahiyar Afirka, kasar Sin ta taimaka ta shimfida layukan dogon da tsawon su ya zarce kilomita dubu 6, da hanyoyin mota da tsawon su shi ma ya zarce kilomita dubu 6, da gina wasu tashoshin jiragen ruwa kusan 20, da kafa wasu manyan na’urorin samar da wutar lantarki fiye da 80. Har wa yau, kasar Sin ta kasance aminiyar ciniki mafi girma ga Afirka a cikin jerin shekaru 13, kuma kudin cinikayyar bangarorin biyu ya kai dala biliyan 282 a shekara ta 2022. Duk wadannan nasarorin da aka samu tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, ba taimakawa ci gaban Afirka kadai suka yi ba, har ma sun kara samar da kyawawan sharudda wajen habaka hadin-gwiwa tsakanin sauran kasashe da kasashen Afirka.

A ra’ayin David Monyae, babban darektan cibiyar nazarin Afirka da Sin a jami’ar Johannesburg dake kasar Afirka ta Kudu, kasashen Afirka na kara hada gwiwa tare da kasar Sin bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”, kuma zamanantarwa irin ta kasar Sin, ta samar da babban zarafi, da zama tamkar abun misali ga ci gaban kasashe masu tasowa, ciki har da na Afirka.

Tun barkewar annobar COVID-19, ya zuwa yanzu, Sin da Afirka na kara baiwa juna taimako da goyon-baya. Lokacin da kasar Sin take cikin mawuyacin hali na tinkarar annobar, a watan Fabrairun shekara ta 2020, majalisar ministocin kungiyar tarayyar Afirka wato AU, ta fitar da sanarwar marawa kasar Sin baya wajen dakile yaduwar annobar, wadda ta kasance muhimmiyar kungiyar kasa da kasa ta farko dake baiwa kasar Sin goyon-baya. Bayan da annobar ta barke a nahiyar Afirka kuma, ba tare da wani jinkiri ba Sin ta fara samar da tallafin jin-kai ga nahiyar. A ranar 17 ga watan Yunin shekara ta 2020, shugaba Xi Jinping ya jagoranci taron koli na musamman kan hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin yaki da annobar COVID-19, inda ya sanar da cewa, “Sin za ta fara aikin gina hedikwatar cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afirka wato Africa CDC a cikin shekara ta 2020”, kana “za’a fara baiwa kasashen Afirka alluran riga-kafin cutar COVID-19 da zarar kasar Sin ta kammala aikin samar da su”.

A watan Janairun shekarar da muke ciki, an kammala aikin gina hedikwatar cibiyar Africa CDC a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, inda mataimakiyar shugaban kwamitin kungiyar AU, Madam Monique Nsanzabaganwa ta ce, kwalliya ta biya kudin sabulu, a fannin inganta hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afrika a bangaren kiwon lafiya, abun da ya shaida cewa, kasar Sin ta kai ga cika alkawarin da ta dauka.

Muna sa ran ganin cewa, a sabon zamanin da muke ciki, a karkashin jagorancin shugabannin kasar Sin da kasashen Afirka, za’a kara raya al’ummomin bangarorin biyu masu kyakkyawar makoma ta bai daya, da bayar da sabuwar gudummawa ga samar da ci gaban daukacin al’ummun duniya. (Murtala Zhang)