logo

HAUSA

Zhao Yingxin: kwararriyar mai daukar hoton wasanni ta kasar Sin (B)

2023-05-22 15:08:12 CMG Hausa

Zhao Yingxin, ita ce mataimakiyar shugabar kungiyar mata masu daukar hoto ta kasar Sin kuma shugabar Jaridar yada labarai ta hotuna ta kasar Sin. Yayin wasannin Olympics na Beijing a 2008, Zhao ta zama mace ta farko da ta rike matsayin shugabar masu daukar hoto a tarihin wasannin Olympics na duniya. Haka kuma, ita ce ‘yar kasar Sin ta farko da ta samu wannan matsayi. A 2022, Zhao ta adana gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ta Beijing ta hanyar kyamararta, kuma ta shaida gasannin wasannin Olympics guda biyu da Beijing ta karbi bakuncinsu ta hanyar kyamararta. 

Zhao Yingxin ta fara sha’awar wasan kwallon tebur a lokacin da take makarantar firamare, daga nan ne kuma ta fara kaunar wasannin motsa jiki.

Ta karanci bangaren daukar hotunan yada labarai a lokacin da ta yi dalibta a sashen nazarin aikin jarida na jami’ar Renmin a Beijing. Bayan ta kammla, ta zama mai daukar hoto dake aiki da kamfanin dillancin labarai na Xinhua. A shekarar 1993, ta fara aiki a kasar Birtaniya a matsayin mace mai daukar hoto ta farko da Xinhua ya tura ketare.

Yayin da take aiki da Xinhua, ta dauki hotunan muhimman lokuta da dama, kamar na dawowar yankin Hong Kong karkashin ikon kasar Sin, da cikar jamhuriyar jama’ar kasar Sin shekaru 50 da kafuwa, da damar da Beijing ya samu na karbar bakuncin wasannin Olympics, da wasannin Olympics na lokacin hunturu na birnin Salt Lakes a 2002, da wasannin Olympics na Athens a shekarar 2004. Ta kan dauki kayayyakin daukar hoto kamar takwarorinta maza, kuma tana daukar hotuna masu kyau da inganci kamarsu. Zhao ta ce, “zan iya aiki da kyau kamar yadda maza za su yi ko ma fiye da su. Ta hakan ne kawai za a samu sabbin masu ban mamaki.”

A ganinta, mata masu daukar hoto sun fi mayar da hankali fiye da maza. A ko da yaushe, Zhao na son daukar hoton idanun ‘yan wasa yayin da ake fafatawa a gasa, saboda idanunsu za su fi taba zuciyar ‘yan kallo. “Daukar hotuna yayin da ake tsaka da fafatawa a gasa, shi ne zai bayyana irin karfin zuciyar ‘yan wasa”, cewar Zhao.

A ganin wasu mutane, a wasu lokuta a kan yi rashin nasarar daukar hoto yayin wasannin Olympics, saboda lokaci ne da ba zai maimaitu ba. Amma wannan shi ne sirrin zama mai daukar hoton wasannin, saboda ana yin wasannin ne kai tsaye, don haka dole ne mai daukar hoto ya mayar da hankali matuka domin daukar hotunan lokuta mafiya kayatarwa. A sana’arta, Zhao ta ga kayatattun lokuta, da masu taba zuciya da ma wadanda suka shiga tarihi.

Chen Lu ta kasance zakarar wasan zamiyar kankara na Figure Skating na farko a kasar Sin. Zhao ce kadai basiniya mai daukar hoto a wajen, a lokacin da Chen ta lashe lambar zinare a gasar zakarun duniya na zamiyar kankara a 1995, a Birmingham na Birtaniya. Zhao ta dauki hoton idanun Chen a lokacin da take farin cikin lashe lambar yabon.

Shekaru 17 bayan nan, Zhao ta halarci wasannin Olympics na lokacin hunturu na birnin Salt Lake a shekarar 2002, kuma ta shaida wani muhimmin tarihi a lokacin da Yang Yang ta lashe lambar Zinare na farko a wasannin Olympics na tseren kan kankara na gajeren zango mai mita 500. Zhao ta tuna da idanun Yang Yang a lokacin da take fafatawa a matakin karshe na gasar. Abun da Zhao ta gani a idanun Yang, wani irin kuzari ne na kokarin cimma burinta na wasannin Olympics, da kuma ainihin ruhin wasannin na Olympics.

Zhao ta ce, “a shekarun da na dauka ina daukar hotuna, ba shaida raunikan da ‘yan wasa suka ji kadai na yi ba, har ma da irin kuzari da karsashin da suke da shi ga wasanni. Bayan daukar hotunan wasannin Olympics, na kara fahimtar ruhin wasannin.”

Zhao wadda a baya daliba ce, da ke kaunar wasan kwallon tebur kuma mai daukar hotunan wasanni, kana shugabar masu daukar hotunan wasannin Olympics, ta kasance mai samun kwarin gwiwa daga ruhin wasanni. Ba ta taba yin kasa a gwiwa a kokarinta na samun ci gaba ba. Littafinta na First Woman Photo Chief in Olympic History, ya bayyana aikin da ta yi a matsayin shugabar masu daukar hotunan wasannin Olympics da kuma aikinta a matsayin mai daukar hoto. Ta hanyar labaran da ta bayar, littafin ya zayyana gwagwarmayar wani zamani.

Lokaci na sauyawa, kuma Zhao ma na sauyawa. Amma kaunarta ga wasanni, da daukar hoto da ma jajircewarta wajen cimma burin aikinta, ba za su taba sauyawa ba. Ta yi ammana cewa, daukar hoto da yadda hoton ke jan hankali da ma aikewa da sako, zai taka muhimmiyar rawa wajen adana tarihi da ma inganta ci gaban al’umma.

A zamanin da hotuna suka yi fice, fasaha za ta iya sauya yadda ake daukar hotuna da adana su, kuma za ta iya saukaka aikin daukar hoto, amma kuma ba za a taba maye gurbin zuciya da basirar kwararren mai daukar hoto ba.

Zhao na fatan karin masu daukar hoto za su taimaka wajen amfani da kyamarorinsu domin adana tarihin wannan muhimmin zamani, kuma za su taimakwa wajen samar da ingantattun hotuna (Kande Gao)