logo

HAUSA

Xi Jinping Ya Jagoranci Taron Koli Tsakanin Kasar Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya

2023-05-20 18:11:05 CRI

Yau Jumma’a da safe ne aka bude taron kolin kasar Sin da kasashen Tsakiyar Asiya karo na farko a birnin Xi'an, babban birnin lardin Shaanxi da ke tsakiyar kasar Sin, inda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jagoranci taron, tare da gabatar da jawabi:

 

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya gabatar da ra'ayinsa kan yadda za a raya yankin tsakiyar Asiya, inda ya ce, tilas ne a kiyaye ikon mulki da tsaro, da 'yanci da cikakkun yankunan kasashen yankin tsakiyar Asiya, kana a girmama hanyar da al'ummomin kasashen suka zaba da kansu wajen raya kasa, a goyi bayan kokarin yankin na samun zaman lafiya, jituwa da kwanciyar hankali.

Ban da haka kuma, shugaban na kasar Sin ya gabatar da shawarwari guda 8 kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen tsakiyar Asiya, wato kara kafa tsare-tsare, kyautata huldar tattalin arziki da ciniki, zurfafa hadewar juna, kara yin hadin gwiwa ta fuskar makamashi, kara azama kan yin kirkire-kirkire maras gurbata muhalli, inganta karfin bunkasuwa, kara yin tattaunawa ta fannin harkokin al'adu, da kiyaye zaman lafiya a yankin.