logo

HAUSA

Sharhi: Kasashen duniya za su gano amsa in sun kwatanta tarukan koli na Xi’an da Hiroshima

2023-05-20 22:12:38 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

A kwanakin nan, an gudanar da manyan tarukan koli guda biyu kusan a lokaci guda, wato taron kolin kasar Sin da kasashen da ke tsakiyar Asiya wanda aka gudanar a birnin Xi’an na kasar Sin, birnin dake zama mafarin hanyar siliki, da kuma taron kolin kungiyar G7, wanda aka gudanar a birnin Hiroshima, birni na farko a duniya da aka kai masa harin nukiliya, hakan nan kuma tarukan biyu sun bambanta sosai bisa la’akari da abubuwan da suke neman cimmawa.

Taron kolin kasar Sin da kasashen da ke tsakiyar Asiya wanda aka kammala shi ba da jimawa ba, ya mai da hankali a kan karfafa hadin gwiwa don tinkarar kalubale, kuma manufar taron shi ne karfafa hadin kai a maimakon yin fito na fito. Kamar dai yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a jawabinsa cewa, duniya na fatan ganin tabbatar da kwanciyar hankali da ci gaba da jituwa da hadewa da juna a tsakiyar Asiya, ya kamata a gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a tsakanin Sin da kasashen da ke tsakiyar Asiya, kuma ya kamata kasashen su tsaya kan taimakon juna da tabbatar da ci gaban juna da tsaronsu na bai daya da sada zumunta da juna daga zuriya zuwa zuriya. Haka nan kuma ya shaida yadda kasar Sin ke cudanya da kasashen biyar din da ke tsakiyar Asiya bisa tushen zaman daidaito, kuma ba domin dakile wata kasa ba suke hulda da juna. Taron na yini biyu ya cimma gagaruman nasarori, kuma babu shakka ya shaida ainihin ma’anar cudanyar kasa kasa, tare da kiyaye tsari da adalci a duniya.

A daya bangare kuma, taron kolin G7 da har yanzu ke gudana a birnin Hiroshima, yana mai da hankali a kan haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin kasashen duniya, wato su kulla kawance don yin fito na fito da wasu kasashe. Kasar Japan mai masaukin baki tana amfani da damarta ta karbar bakuncin taron, don neman kulla kawance da sauran kasashen kungiyar, a yunkurin tinkarar abin da take kira wai “barazana daga Rasha da Sin da kuma Koriya ta arewa”, a sa’i daya kuma, tana neman goyon baya daga kawayen nan nata a kan batun zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin tekun Pasifik. Ita kuma kasar Amurka ma burinta a bayyane ne, wato tana ci gaba da neman rura wutar rikicin Ukraine, tare da karfafa kawancenta da kasashen G7 wajen tinkarar kasar Sin. Da haka, muke iya gano cewa, manufar taron G7 shi ne su karfafa kawancensu don dakile sauran kasashe.

In mun kwatanta tarukan biyu, cikin sauki za mu gane cewa, tarukan biyu sun bambanta sosai daga dalilan gudanar da su da ma burin da ake neman cimmawa. Taron da aka gudanar a birnin Xi’an an gudanar da shi ne sabo da neman ci gaba na bai daya, don haka ma, abin da aka tattauna a gun taron shi ne ta yaya za a tabbatar da ci gaban kasashen. A sa’i daya kuma, taron da aka gudanar a Hiroshima ya shaida yadda kasashen G7 suke da ra’ayin nan na samun ci gaba daga faduwar wani, don haka ma, sun fi mai da hankali a kan yadda za su kulla kawance da juna don yin fito na fito da wasu.

Daga Xi’an zuwa Hiroshima, tarukan biyu tamkar wani madubi ne dake haskakawa kasashen duniya, don gano amsa idan sun kwatanta su. (Lubabatu Lei)