logo

HAUSA

Kasar Sin za ta ci gaba da tattaunawa da Poland kan batun warware rikicin Ukraine a siyasance

2023-05-20 16:23:34 CMG Hausa

Wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin kan harkokin Turai da Asiya, Li Hui, ya bayyana cewa, Sin na son ci gaba da tattanawa da kasar Poland kan batun warware rikicin kasar Ukraine ta hanyar siyasa, tare da nuna goyon baya ga kafa daidaitaccen tsarin tsaro mai inganci da dorewa a Turai.

Li ya bayyana hakan ne jiya Jumma’a, a lokacin da yake ganawa da mataimakin ministan harkokin wajen Poland Wojciech Gerwel a birnin Warsaw.

Li ya ce, ba burin bangarori ba ne a kara tsawaita rikicin na Ukraine, yana mai cewa, kasar Sin ta yi kira da a sake yin shawarwari na zaman lafiya. Ya kuma kara nanata matsayin kasar Sin kan rikicin, wanda shi ne kyautata shawarwarin zaman lafiya.

Dangane da takardar da ta bayyana matsayinta game da warware rikicin Ukraine da kasar Sin ta fitar a siyasance, Li ya ce, kasarsa za ta karfafa mu'amala da dukkan bangarori, kuma sannu a hankali, za ta tattara ra'ayoyi, don kafa ginshikin tsagaita wuta da kuma dakatar da rikicin.

A nasa bangare Gerwel ya bayyana cewa, kasar Poland za ta yi aiki tare da kasar Sin, wajen ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba. Da yake jinjinawa rawar da kasar Sin ta taka a harkokin kasa da kasa a matsayinta na mamban dindindin a kwamitin sulhu na MDD, ya ce, bangaren Poland na fatan kasar Sin, za ta ci gaba da taka rawar gani a kokarin daidaita rikicin, da sa kaimi ga hanzarta sassauta halin da ake ciki, domin tabbatar da zaman lafiya nan da nan. (Ibrahim)