logo

HAUSA

Dan Damben Boksin Na Sin Zhang Zhilei Ya Lashe Kambin Hukumar WBO

2023-05-19 09:30:44 CMG Hausa

Zakaran damben boksin dan kasar Sin Zhang Zhilei, ya doke takwaransa na Birtaniya Joe Joyce a zagaye na 6, inda da karbe kambin damben hukumar WBO na ajin masu nauyi.

Da yake tsokaci game da nasarar sa, Zhang ya ce "Wannan dambe ne da ya zo min da sauki sama da yadda na yi tsammani. Na yi aiki tukuru kafin karawar amma yanzu na ci gajiyar kwazo na". Zhang wanda zai cika shekaru 40 a wannan wata, ya bar sansanin horon sa dake Amurka zuwa filin wasan dambe na Copper Box Arena dake birnin Landan, inda dubban ‘yan kallo suka rika shewa da murnar ganin karawar sa da Joyce mai shekaru 37. Yanzu haka dai Zhang ya yi nasara a wasanni 15 a jere.

Kafin fara fafatawar, magoya bayan Joyce sun rika daga murya suna jinjina masa, amma duk da haka, ya sha kaye tun daga zagayen farko na karawar, inda ya rika shan naushi daga Zhang, har zuwa zagaye na 6, inda Zhang din ya samu nasara a kan sa.

Joyce wanda ke rike da lambar azurfa ta gasar Olympic da aka gudanar a birnin Rio na Brazil a shekarar 2016, ya rika tangadi yayin da yake shan naushi daga Zhang, kuma jini ya rika fita daga fuskarsa, har zuwa lokacin da alkalin damben ya tsayar da wasan a zagaye na 6, ya kuma baiwa Zhang nasara. Yanzu haka dai Zhang din ya maye gurbin Joyce, a matsayin wanda zai yi takara da zakaran dambe ajin masu nauyi na duniya karkashin hukumar Boksin ta WBO, wato Oleksandr Usyk dan asalin kasar Ukraine.

Zhang ya ce "Ina godewa mai horas da ni, da ‘yan tawaga ta, da masu mara min baya daga Sin, wadanda suka jira har tsakar dare domin su kalli wasa na. Wannan tamkar kyautar bikin ranar haihuwa ta ne mafi daraja, daga ‘yan tawaga ta da ni kai na".

Duk da nasarar da ya samu, a yanzu Zhang na fatan cimma nasarar lashe kambin duniya, ya kuma bayyana cewa, ba shi da niyyar hutawa mai tsawo, har sai ya kai ga cimma burin sa na lashe babban kambin na duniya baki daya.

Bayan da Zhang Zhilei ya lashe kambin hukumar WBO, ya kasance dan kasar Sin na farko da ya lashe wannan kambi a gasar dambe ta duniya. Ana iya cewa, Zhang Zhilei ya kafa tarihi, nasarar da ya samu tana da babbar ma’ana, masu sha’awar wasan dambe na kasar Sin sun taya shi murna sosai. Ba ma kawai Zhang Zhilei ya yi suna a tsakanin masu sha’awar wasan dambe ba, har ma ya yi suna a tsakanin al’ummar kasar Sin. Koda yake Zhang Zhilei zai cika shekaru 40 da haihuwa, ya yi tsufa kadan a tsakanin ‘yan wasan dambe, amma ya na da kuzari sosai, kuma ya yi namijin kokari don cimma zakara a kambin duniya.

Zhang Zhilei ya taba samun lambar azurfa a wasan dambe na gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008, kuma ya shiga dandalin dambe na hukumar WBO a shekarar 2014. Zhang Zhilei yana begen yin takara da zakaran dambe ajin masu nauyi na duniya karkashin hukumar Boksin ta WBO, wato Oleksandr Usyk.

Yayin da aka waiwayi wasan da Zhang Zhilei ya lashe, Zhang yana kwantar da hankali a maimakon farin cikin sosai, ya bayyana cewa, lokacin da ya lashe wasan, bai ji komai a cikin zuciyarsa ba, a ganinsa wannan sakamako ne da ya kamata ya samu. Shi da tawagarsa dukkansu sun yi kokari sosai, sun samu irin nasara, kuma sun gamsu sosai.

Kafin wasan, mutane da dama sun yi tsammani Joyce zai lashe wasan, domin shi ne mafi kuruciya, kana ya kai matsayi na farko a hukumar WBO, kuma matsayi na hudu a dandalin wasan na duniya, amma Zhang Zhilei ya na bayan matsayi na 20 a duniya a lokacin.

Zhang Zhilei ya bayyana cewa, bai damu da matsayinsa na wasan a duniya ba, koda yake matsayi ya zarce 100, idan kwarewa ta cika to babu matsala. Kafin wannan gasa, ya shirya sosai, ya yi imanin zai cimma nasara. A kusan budewar gasar, ya kwantar da hankali, da jiran budewar gasa. Zhang Zhilei ya shaida karfinsa a wasan.

Zhang Zhilei ya bayyana cewa, burinsa shi ne lashe babban kambin na duniya. Tun da ya shiga dandalin hukumar WBO a shekarar 2014, yayi kokarin neman cimma wannan buri har na tsawon shekaru kimanin 10, yanzu dai ya kusan cimmawa. Ya ce, nasarorin da ya samu a halin yanzu sun zo daga kokarinsa a lokacin da. A farkon shekaru 10 wato lokacin da ya fara koyon wasan dambe a shekarar 1998 zuwa lashe lambar yabo ta azurfa a gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008, ya cimma burinsa na farko, yanzu dai, ya sa kaimi ga kansa don cimma burinsa na wadannan shekaru 10.

An haife shi a kauyen Shenqiu dake birnin Zhoukou na lardin Henan, lokacin da ya shiga makarantar midil, an shigar da shi zuwa kungiyar wasan tseren kwale-kwale ta garinsu. Dama Zhang Zhilei zai ci gaba da horo a wasan tseren kwale-kwale, amma tsayin jikinsa ya kai mita 1.9 yayin da shekarunsa ya kai 12 da haihuwa, don haka bai dace da wasan ba domin tsayinsa. Sai aka ba shi shawarar koyon wasan dambe. Don haka, mahaifinsa ya jagorance shi zuwa kungiyar wasan dambe ta lardin Henai, kuma nan da nan mai horaswa na kungiyar ya yi sha’awar shigar da shi cikin kungiyar.

Bayan da ya shiga kungiyar, ya fara yin horo a kowace rana. Kullum ya tsaya a gaban madubi har na tsawon wasu awoyi don gyara jikin yin wasan dambe. A wasu lokuta, kafafunsa suna kangarewa har ba ya iya motsi. Ya ci gaba da yin kokarin horo har ya samu sakamako mai kyau. Zhang Zhilei ya yi gasa ta farko tare da zakaran wasan dambe na lardin Henan. Bayan budewar gasar, bai san yadda zai yi ba, babu wani abu da yake tunani. Bayan mintuna biyu kawai, sai ya ji gajiya sosai har ma ya kwanta a wurin wasan. Amma bai ji tsoro ba, mai horaswa ya gaya masa cewa, za a yi gwajin jaruntakarsa ta wannan gasa, don haka ya nuna jarumtaka sosai.

A shekarar 2001, Zhang Zhilei ya zama matsayi na uku na wasan dambe mai nauyin fiye da kilogram 91 a gasar wasannin motsa jiki ta kasar Sin karo na 9. Kana ya cimma zakara a wasan a gasar wasannin motsa jiki ta kasar Sin karo na 10 a shekarar 2005. Kuma a shekarar 2008, Zhang Zhilei ya halarci gasar wasannin Olympics ta Beijing, inda ya samu lambar yabo ta azurfa. A ganinsa, ya zama kamar matsayin koli a wasan. Yana son ci gaba da cimma zakara a gasar wasannin Olympics ta London ta shekarar 2012, amma bai samu nasara ba. Saidai bayan da ya gama halartar gasar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ta shekarar 2013, sai ya janye daga dandalin wasan na kasar Sin.

A shekarar 2014, Zhang Zhilei ya zabi tafiya kasashen waje da kasance dan wasan hukumar WBO. yana son ciyar da kansa da tawagarsa ta wasan gaba, har ma yana son cimma matsayin kan gaba a duniya. Game da dalilin da ya sa Zhang Zhilei ya zabi zama dan wasan hukumar WBO, ya bayyana cewa, ya riga ya halarci gasar wasannin Olympics sau biyu, kuma idonsa ya bude sosai. Yayin da yake samun horo kan wasan dambe, ya kan kalli gasannin hukumar WBO kamar su Mike Tyson da Lennox Lewis, don haka yana son shiga hukumar WBO da ganin yadda ake buga wasan dambe a dandalin wasan mafi kyau na duniya.

Amma ba abu ne mai sauki gare shi ba yayin da yake wasan a kasar Amurka. Lokacin da ya fara yin wasan a kasar, ya dauka za a dauke shi a matsayin dan wasan da ya samu lambar yabo ta azurfa ta gasar wasannin Olympics, amma a hakika dai, babu wanda ya tuna da wannan sakamako, sun fi son ganin wanda ya fi kwarewa kadai.

A wadannan shekaru 10 da suka gabata, Zhang Zhilei ya yi rayuwa mai wuya. Ya zama daga dan wasan kungiyar wasan dambe ta kasar Sin zuwa dan wasan dandalin hukumar WBO, da farko dai bai saba da irin rayuwa wato jagorantar kansa da tawagarsa duka ba. Zhang Zhilei ya bayyana cewa, kudin dan wasan hukumar WBO na zuwa ne bayan da aka yi gasa. Da farko dai, kudinsa ya yi kadan, saidai idan ya yi gasanni da dama. Ya ce, ba ya iya biyan kudin rancen gida da mota a lokaci mafi wuya.

Zhang Zhilei ya yi rayuwa mai wuya a lokacin da, amma ya saba da ita, kullum ya kan yi bayani game da kaunarsa kan wasan dambe, ba tare da  ambato wahalar da ya sha a kan wasan ba. A hakika, ya ji rauni da dama a jiki. An yi tiyata da dama kan jikinsa.

Koda yake Zhang Zhilei ya kan waiwayi rayuwarsa mai wahala a wasu lokuta, a halin yanzu hankalinsa a kwance yaje yayin da yake bayani game da rayuwarsa. Ya ce, ya manta wahalar da ya sha, ya maida ita a matsayin muhimmin kashi na rayuwarsa, wadda ta sa kaimi gare shi wajen samun ci gaba a nan gaba.(Zainab Zhang)