Kyawawan sakamakon tattalin arziki, da cinikayya da aka samu a tsakanin kasar Sin da kasashen dake tsakiyar Asiya
2023-05-18 07:55:38 CMG Hausa
Assalamu alaikum, masu kallonmu. A gobe ne za a kira taron koli na kasar Sin da kasashen dake tsakiyar Asiya a birnin Xi’an. A cikin shirinmu na yau, zan gabatar muku kyawawan sakamakon tattalin arziki, da cinikayya da aka samu a tsakanin bangarorin biyu, bisa shawarar Ziri daya da hanya daya.
An gabatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya” wato Belt and Road Initiative a shekarar 2013, bisa manufar sa kaimi ga ci gaba, da wadatar kasashen da ke kan hanyar siliki ta hanyar raya cinikayya, zuba jari da raya ababen more rayuwa.
Tun bayan da kasashen da ke tsakiyar Asiya, wato Kazakhstan, Uzbekistan, Tajikistan, Turkmenistan, da Kyrgyzstan suka sa hannu kan shawarar ziri daya da hanya daya, sun samu sakamako na a zo a gani, ta hanyar hadin gwiwa tare da kasar Sin a cikin shekaru 10 da suka gabata.
A cikin shekaru 10n, aikin jigilar kayayyaki ta layin dogo a tsakanin Sin da Turai, da ma sauran kasashen da shawarar ta shafa ya samu bunkasa sosai. Ya zuwa karshen shekarar 2022, ana amfani da layin dogon sau dubu 65 wajen jigilar kayayyaki, kana kaso 80 daga cikinsu sun ratsa yankin tsakiyar Asiya.
Ban da wannan kuma, ya zuwa karshen watan Maris na bana, yawan kudin da kasar Sin ta zuba wa kasashen da ke tsakiyar Asiya kai tsaye, ya zarce dalar Amurka biliyan 15, kana ayyukan hadin kansu sun shafi fannonin kere-kere, da sadarwa, da tattalin arziki ta yanar gizo da dai sauransu.
A shekarar 2022, jimillar cinikayya a tsakanin bangaron biyu sun kai dala biliyan 70.2, inda jimillar cinikayya a tsakaninsu ta yanar gizo ta karu da kaso 95.
Kasar Sin ta kasance abokiyar kasuwanci mafi muhimmanci ta kasashen biyar dake tsakiyar Asiya a jerin shekarun da suka wuce.