logo

HAUSA

Sin na fatan sassan da rikicin Ukraine ya shafa za su gaggauta amincewa juna

2023-05-18 20:03:18 CMG Hausa

Wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin game da harkokin da suka shafi Turai da Asiya Li Hui, ya jaddada bukatar gaggauta amincewa juna tsakanin kasashen da rikicin Ukraine ya shafe, kana a samar da wani yanayi da zai ba da damar tattaunawar samar da zaman lafiya.

Wata sanarwa da ma’aikatar wajen Sin ta fitar a yau Alhamis, ta ce Li Hui ya yi kiran ne yayin ziyarar yini biyu da ya gudanar a Ukraine, inda ya gana da shugaban kasar Volodymyr Zelenskyy, tare da gudanar da tattaunawar musamman da ministan harkokin wajen kasar Dmytro Kuleba, da karin wasu manyan jami’an gwamnatin Ukraine din.

A cewar Li, “Ba wata hanya daya tilo ta magance rikicin kasar baki daya”, don haka ya bukaci dukkanin sassan da batun ya shafa, da su ba da ta su gudummawar, wajen samar da amincewar juna, da kafa yanayin saukaka dauki-ba-dadin da ake yi, da kuma komawa shawarwarin wanzar da zaman lafiya. (Saminu Alhassan)