logo

HAUSA

Matsalar Kasa Biyan Basusukan Da Amurka Take Fuskanta Za Ta Kawowa Duniya Asara

2023-05-18 18:51:55 CMG HAUSA

DAGA MINA

Abokai, ofishin kula da kasafin kudi na majalisar dokokin kasar Amurka ya ba da wani rahoto, wanda ya shaida kashedin da sakatariyar kudin kasar Janet L. Yellen ta yi kan matsalar kasa biyan basusuka da kasar za ta fuskanta, abin da ya bayyana cewa, kila a ran 1 ga watan Yuni, Amurka za ta sabawa yarjejeniyar.

Amurka ta dade tana amfani da basussukan da ake bin ta don cika gibin kudaden gwamnati. A hakika, tun daga shekarar 1939 zuwa yanzu, majalisar dokokin kasar ta daga iyakar yawan basusukan da kasar ke iya ci har da sau dari, wato daga dala biliyan 45 zuwa dala triliyan 31.4. Amurka ta kasance kasa mafi karfi a duniya dake da basussuka masu dimbin yawa, inda ma’auninta na CDS, wato ma’aunin yiwuwar kasa biyan bashi, ya wuce na kasashen Girika da Peru da dai sauran wasu kasashe, kuma ja-in-ja tsakanin jam’iyyun kasar biyu shi zai iya jefa kasar cikin rikicin kasa biyan basussuka. In dai hakan ya faru, za a sayar da basusukan da ake bin Amurka, matakin da zai haifar da hauhawar farashin kudin ruwa da raguwar darajan kudin dala, kuma bankuna da dama za su yi fama da fatarar kudi, darajar hannayen jari ma za ta ragu ainun. Ba shakka, hakan zai kawowa tattalin arzikin duniya, masamman ma tattalin arzikin kasashe masu tasowa kalubale, a karshe kuma, al’ummar duniya za su yi asara. (Mai zana da rubuta: MINA)