logo

HAUSA

Kara dasa bishiyoyi a birni yana rage yawan mutuwar mutane sakamakon tsananin zafi

2023-05-17 09:15:05 CMG Hausa

 


Masu nazari sun yi nuni da cewa, kara dasa bishiyoyi a birane yana taimakawa wajen rage zafin yanayi a lokacin zafi, tare da rage yawan mutuwar mutane sakamakon tsananin zafi.

Wannan rahoton da aka wallafa cikin mujallar Lancet ta kasar Birtaniya ya yi bayani da cewa, masu nazarin sun fitar da wani tsarin hasashen  fa'idodi masu kyau da kara dasa bishiyoyi a birane yake haifawa, inda suka gano cewa, idan an kara fadin gandun daji a birane zuwa kaso 30 cikin dari bisa jimillar fadin birnin, to, za a rage matsakaicin zafin yanayi da digiri Celsius 0.4 a lokacin zafi.

Masu nazarin sun bayyana cewa, a cikin birane guda 93 da ke nahiyar Turai, tsananin zafi ya haddasa mutuwar wuri ga mutane dubu 7 da dari 7 a shekarar 2015, a cikinsu kuma wasu kashi 1 cikin kashi 3 ne da ma za su tsira daga mutuwa. Yanzu matsakaicin fadin gandun daji bai kai kaso 15 cikin 100 bisa jimillar fadin biranen Turai ba.

A shekarar 2022 ne an yi fama da tsananin zafi sau da dama a kasashen Turai, inda zafin yanayi ya kafa tarihi a wasu kasashen. Hukumar kula da hidimar sauyin yanayi ta Copernicus karkashin inuwar kungiyar tarayyar Turai ta gabatar da rahoto a watan Satumban shekarar 2022 cewa, lokacin zafi na shekarar 2022, lokaci ne mafi zafi a tarihin nahiyar Turai.

Dangane da alakar da ke tsakanin tsananin zafi da kuma matsalar lafiyar al’umma, madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin haske da cewa, mai yiwuwa tsananin zafi ya haifar da lalacewar zuciya da huhu, da kwanciya a asibiti da kuma mutuwar wuri.

Manazatan sun yi bayani da cewa, kullum a lokacin zafi, zafin yanayi a birane ya fi na wuraren da ke kawayensu da kuma yankunan karkara yawa. Dalilan da suka sa haka su ne, domin rashin isassun bishiyoyi, iskar da na'urorin sanyaya daki suke fitarwa, da kayayyakin gine-gine da kwalta mai launin baki wadanda ke karbar hasken rana.

Wasu nazarce-nazarcen da aka gudanar a baya sun nuna cewa, wuraren da aka dasa yawan bishiyoyi da ciyayi a birane, sun amfana wa jikin al’umma da kuma tunaninsu, kana sun kare su daga kamuwa da ciwon magudanar jini a zuciya da kwakwalwa da cutar karancin basira, tare da kyautata kwarewar kananan yara da tsofaffi ta fannin fahimta. (Tasallah Yuan)