Hadin gwiwar Sin da Eritrea ya haifar da tarin alherai
2023-05-17 10:18:41 CMG Hausa
A yanzu haka shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki, na gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin, ziyarar da ta ba shi damar ganawa kai tsaye da shugaban kasar Xi Jinping, da kuma firaministan Sin Li Qiang.
Yayin zantawarsu a ranar Litinin, shugaba Xi ya tabo irin nagartar dangantakar sassan biyu, ta yadda cikin shekaru 30 da kulla huldar diflomasiyya suke ci gaba da goyon bayan juna, da kasancewa juna kawaye na-gari masu iya dogaro da juna.
Kaza lika, shugaban na Sin ya kara jaddada aniyar kasarsa ta bunkasa hadin gwiwa da Eritrea, duk kuwa da sauye-sauyen da duniya ke fuskanta, matakin da a cewarsa zai tallafawa kasashen biyu, da ma shiyyoyinsu a fannin wanzar da zaman lafiya da daidaito.
Ko shakka babu kasar Sin ta jima tana aiwatar da matakai daban daban, na kare ikon mulkin kan kasashen Afirka ciki har da Eritrea, tana kuma goyon bayan kasashen nahiyar bisa hanyoyin da suka zaba na ciyar da kai gaba, tare da nuna adawa da matakan tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran sassa.
Kaza lika, Sin na fatan Eritrea da sauran kasashen Afirka, za su rungumi salon cudanyar kasa da kasa bisa doka, su kuma yi aiki tare domin “A Gudu Tare A Tsira Tare”.
A nasa bangare shugaban Eritrea Isaias Afwerki, ya jinjinawa shawarwarin da kasar Sin ta gabatar domin ci gaban kasashen duniya, ciki har da shawarar “ziri daya da hanya daya”, da dandalin bunkasa hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, da shawarar bunkasa zaman lafiya da ci gaban yankin kahon Afirka.
Shugaba Afwerki ya kuma yi fatan Sin za ta ci gaba da tallafawa Eritrea a fannin zuba jari, da habaka cinikayya, da karfafa hadin gwiwar samar da ababen more rayuwa, da raya sha’anin sadarwa, da noma da hakar ma’adanai, za ta kuma ci gaba da aikewa da kwararru a fannin noma zuwa Eritrea.
A zantawar shugaban na Eritrea da firaministan Sin Li Qiang kuwa, firaministan ya jinjinawa aminci a fannin siyasa, da hadin gwiwa dake tsakanin kasarsa da Eritrea, tare da fatan gwamnatin Eritrea za ta ci gaba da raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin sassan biyu, da kuma dorewar hadin gwiwa mai ma’ana, na cimma moriyar juna tsakanin sassan biyu. (Saminu Hassan, Faeza Mustapha, Sanusi Chen)