logo

HAUSA

Magana maras dacewa ta jakada Brigety na tare da wani makasudi

2023-05-16 19:44:55 CMG Hausa

A kwanan baya, Reuben Brigety, jakadan kasar Amurka a kasar Afirka ta Kudu, ya zirgi Afirka ta Kudu da samar da makamai ga kasar Rasha a watan Disamban bara, inda ya ce ya rantse da ransa, abun da ya fada da gaske ne. Lamarin ya janyo hankalin mutanen duniya, inda shugaban kasar Ukraine da ministar harkokin waje ta kasar Jamus suka fadi ra’ayoyinsu dangane da batun. Sai dai abun da ya abku daga bisani ya nuna cewa, hakika mista Brigety ba shi da wata takamaimiyar shaida.

Bayan da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ji zargin da Mista Brigety ya yi wa kasarsa, ya ce bai ji dadin zance maras dacewa da jami’in ya fada ba. Daga baya, ma’aikatar kula da huldar kasa da kasa da hadin gwiwa ta kasar Afirka ta Kudu ta kirawo jakadan na kasar Amurka don yin musayar ra’ayi tare da shi, kana ma’aikatar ta sanar da cewa, Mista Brigety ya yarda da cewa ya yi kuskure, kana ya roki gafara daga gwamnatin kasar Afirka ta Kudu, da jama’ar kasar.

Shi mista Brigety da kansa ma ya sanar a shafin sada zumunta cewa, ya daidaita bahaguwar fahimtar da aka yi kan maganar da ya fada. Sa’an nan, Madam Naledi Pandor, ministar kasar Afirka ta Kudu mai kula da ayyukan huldar kasa da kasa da hadin gwiwa da sauran kasashe, ta tattauna da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Tony Blinken ta wayar tarho. Kana cikin sanarwar da ofishin mista Blinken ya gabatar daga bisani, an jaddada muhimmancin huldar dake tsakanin kasashen nan 2, amma ba tare da yin wani bayani kan zancen mista Brigety ba. Yadda bangaren Amurka ya mayar da martani cikin wani yanayi na kan-kan da kai ya nuna cewa jami’an kasar Amurka sun san kuskurensu. A zahiri ne, yadda jakadan kasar ya yi zargi ba tare da wata shaida ba, har ma ya yi takama cewa zai rantse da rai, bai dace ba ko kadan.

Sai dai an yi zance maras dacewa ne saboda rashin lura? Ko kuma domin wani yunkuri na musamman?

Kamar yadda jaridar Daily Maverick ta kasar Afirka ta Kudu ta bayyana, a watan Faburairun bana, kusan lokacin da sojojin ruwan kasashen Afirka ta Kudu, da Rasha, da Sin suka yi atisaye cikin hadin gwiwa, a yankin teku na kasar Afirka ta Kudu, kasar Amurka ta riga ta gabatar da zargi kan gwamnatin kasar Afirka ta Kudu cewa, ta kwashe wasu makamai cikin wani jirgin ruwan dakon kaya ta kasar Rasha a watan Disamban bara. A sa’i daya, wasu ’yan majalisun kasar Amurka sun bukaci a sake tantance ikon kasar Afirka ta Kudu na halartar shirin dokar tabbatar da karuwar tattalin arziki da damammaki ga kasashen Afirka (AGOA). Wannan shirin doka ya sa kamfanonin kasar Afirka ta Kudu samun gatanci, yayin da suke sayar da kayayyaki zuwa kasar Amurka.

A lokacin, wato watan Faburairu na bana, gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta musunta zirgin da aka yi mata, ta kuma yanke shawarar kaddamar da bincike kan lamarin, gami da tura jami’i mai ba da shawara kan harkar tsaron kasa Sydney Mufamadi zuwa kasar Amurka don tattaunawa da mu’amala da jami’an kasar. Sai dai maganar da jakada Brigety ya fada a wannan karo, ta sa bangaren Afirkta ta Kudu bakin ciki, ganin tamkar kokarin da ta yi na neman daidaita huldar dake tsakaninta da kasar Amurka ya bi ruwa.

A lokacin da mista Mufamadi ke ziyara a kasar Amurka, ya yi kokarin kare ikon kasar Afirka ta Kudu na ci gaba da cin gajiyar shirin dokar AGOA, kana ya tattauna tare da bangaren Amurka dangane da shirin dokar da majalisar wakilan kasar ta zartas a bara, mai taken “Shirin dokar hana kasar Rasha gudanar da munanan ayyuka a nahiyar Afirka”. Makasudin shirin dokar shi ne saka takunkumi kan wasu kamfanoni da kungiyoyi da daidaikun mutane na kasar Rasha, da na wasu kasashen Afirka, don hana kasar Rasha “ zuba jari, da halarta, ko kuma sarrafa harkokin wasu bangarori masu muhimmanci na kasashen Afirka” da “ lahanta moriyar kasar Amurka, da hana ta cimma buri”, wato ana neman hana kasashen Afirka da kasar Rasha yin hadin gwiwa a wasu muhimman harkoki, irinsu hakar ma’adinai, da aikin sadarwa, da aikin soja, da dai sauransu. Har yanzu ba a zartas da shirin dokar a majalisar dattawa ta kasar Amurka ba tukuna. Sai dai idan an zartas da shi, to, zai yi mummunan tasiri kan wasu kasashen Afirka da suke da hulda mai kyau da kasar Rasha, misali kasar Afirka ta Kudu.

Ta hanyar yin tsokaci kan zargin da kasar Amurka ta yi, da wasu shirye-shiryen dokokin da ta gabatar, da lokacin da ta gabatar da su, gami da yadda jakada Brigety ya gabatar da zargi ba tare da wata shaida ba a wannan karo, za a san cewar, dukkan wadannan ayyukan da kasar Amurka ta yi na tare da makasudi guda, wato matsawa kasar Afirka ta Kudu lamba, don hana ta ci gaba da da raya hulda da kasar Rasha. Kana ana neman tsorata sauran kasashe dake nahiyar Afirka, inda tunanin kasar Amurka shi ne, “ Duk wata kasa, ko wata mai karfi kamar Afirka ta Kudu, idan bata bi umarnina ba, to, za a matsa mata lamba, da haifar mata da matsaloli a kai a kai, balle ma sauran kasashe da ba su da karfi.”

Sai dai, manufar kasar Amurka ta babakere, da danniya, da matsawa sauran kasashe lamba, da saka musu takunkumi, ta riga ta zama ruwan dare. Kusan babu wata kasa da ba ta taba shan wahalar manufarta ba. (Bello Wang)