Tchambiano Chaibou: Muna fatan kara hadin-gwiwa tsakanin ‘yan kasuwan Nijar da China
2023-05-16 14:59:05 CMG Hausa
Kwanan baya ne a watan Afrilu, wata tawagar ‘yan kasuwar kasar Sin dake karkashin jagorancin mista Eric Wang Xiaoyong, shugaban kwamitin zartarwa na dandalin kasuwanci na Sin da Afrika da ake kira CABC, ta ziyarci Jamhuriyar Nijar, inda aka gudanar da dandalin zuba jari tsakanin Sin da Nijar a birnin Yamai, a karkashin jagorancin shugaban gwamnatin Nijar, firaminista Ouhoumoudou Mahamadou.
A wajen dandalin, kasar Sin ta bayyana matukar sha’awar ta wajen halartar ayyukan raya tattalin arziki da kyautata rayuwar al’umma a Nijar, da nuna fatan ta ga gwamnatin kasar, da ta ci gaba da kirkiro yanayi mai kyau ga harkokin kasuwanci da zuba jari. Ita kuma gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yi maraba da zuwan tawagar ‘yan kasuwar kasar Sin, da nuna cewa za ta kara bullo da wasu manufofin gatanci don jawo hankalin kamfanonin waje, don su zuba jari da gudanar da kasuwanci a Jamhuriyar Nijar.
Shin ko yaya ‘yan kasuwar Nijar suke kallon wannan zaman taro da kuma wannan dandali na makomar kasuwanci da tattalin arziki na kasashen biyu? Wakilin mu Maman Ada ya tattauna da Tchambiano Chaibou, mukaddashin shugaban ‘yan kasuwa masu shigo da fitar da kayayyaki ta kasar Nijar. (Murtala Zhang/Maman Ada)