Zhao Yingxin: kwararriyar mai daukar hoton wasanni ta kasar Sin (A)
2023-05-15 14:54:02 CMG Hausa
Zhao Yingxin, ita ce mataimakiyar shugabar kungiyar mata masu daukar hoto ta kasar Sin kuma shugabar Jaridar yada labarai ta hotuna ta kasar Sin. Yayin wasannin Olympics na Beijing a 2008, Zhao ta zama mace ta farko da ta rike matsayin shugabar masu daukar hoto a tarihin wasannin Olympics na duniya. Haka kuma, ita ce ‘yar kasar Sin ta farko da ta samu wannan matsayi. A 2022, Zhao ta adana gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ta Beijing ta hanyar kyamararta, kuma ta shaida gasannin wasannin Olympics guda biyu da Beijing ta karbi bakuncinsu ta hanyar kyamararta.
Tsohon shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya IOC, Juan Antonio Samaranch, ya taba cewa, “kafafen yada labarai su ne alkalan karshe na wasannin Olympics. Dole ne mu yi kokarin gamsar da dukkan ‘yan jarida.” ’Yan jarida masu daukar hoto muhimman mahalarta ne kuma masu yada labaran wasannin. Hotunan da suke dauka masu ban sha’awa bisa kwarewa, na yaduwa da kuma ja hankalin duniya. Shugaban masu daukar hoto, matsayi ne mai muhimmanci, saboda mai rike da mukamin ne ke jagorantar kowanne mai daukar hoto dake da rejista, yayin wasannin.
Bisa kundin jagorancin na kwamitin IOC, lallai ne kwamitin ya sanar da sunan shugaban masu daukar hoto, shekaru 3 kafin lokacin wasannin. Kuma dole shugaban ya kasance kwararre a fannin daukar hotunan wasannin kasa da kasa, kuma ya fahimci yadda ayyukan yada labaran wasannin ke gudana, sannan ya kasance mai kwarewa a fannin mu’amala da harkokin shugabanci, kana ya iya Turanci sosai.
A watan Afrilun 2005, shekaru 3 kafin wasannin Olympics na Beijing na 2008, lokacin da kwamitin shirye-shiryen wasannin Olympics na 2008 na Beijing ya yanke shawarar daukar shugaban masu daukar hoto, kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya gabatar da sunan Zhao Yingxin, a lokacin ita ce kwararriyar mai daukar hotunan wasanni ga Xinhua. A don haka, ta zama mace ta farko da ta rike matsayin a tarihin wasannin Olympics.
Zhao ce ke da alhakin kula da harkokin sadarwa da na gudanarwa da na tafiyar da ayyukan da suka shafi daukar hotunan wasannin, ciki har da shirya yadda aikin daukar hotunan wasannin 28 a wuraren wasa 37 za su kasance da kuma kebe wani wuri na musammam ga masu daukar hoto.
Haka kuma, ita ce ke da alhakin dauka da horar da mambobi 80 na tawagar jagororin masu daukar hoto da mataimakansu, da wani ayarin ‘yan sa kai sama da 200. Wadannan mutane sun samu horo kafin a ba su aiki a wuraren wasannin daban-daban.
“Aiki ne mai matukar wahala, dole sai mutum ya shirya sosai,” cewar Anthony Edgar, shugaban sashen yada labarai na kwamitin IOC a wancan lokaci, yayin da ya hadu da Zhao a karo na farko.
Domin tabbatar da gudanar da aikin cikin nasara, Zhao da tawagarta, sun yi iyakar kokarinsu wajen hidimtawa masu daukar hoto yadda ya kamata, kuma sun samu yabo sosai daga masu daukar hoton. A littafinta mai suna, First Woman Photo Chief in Olympic History, wato mace ta farko da ta rike mukamin shugabar masu daukar hoto a tarihin wasannin Olympics, Zhao ta zayyana dalla-dalla, aiki tukuru da ta yi yayin wasannin Olympics na Beijing.
Zhao da tawagarta sun shiga cikin aikin shirya bikin bude wasannin, watanni 6 kafin lokacin gudanar da shi, sun kuma kara fahimtar dukkan batutuwa da abubuwan da suka shafi bikin budewar.
Sun kebe wasu wurare 13 ga masu daukar hoto a wuraren masu sharhin wasannin a filin wasa na Bird’s Nest. Haka kuma, sun tanadi kujeru 300 ga masu daukar hoto a cikin ‘yan kallo, sun kuma kebe wani wuri ga masu daukar hoto a wajen filin wasannin, domin su dauki hotuna daga nesa da za su kunshi kowacce kusurwa, a yayin bikin budewar da na wasannin tartsatsin wuta.
Akwai sadarwar intanet na VLAN a dukkan wuraren da aka kafa domin editoci da masu daukar hoto. An ba masu daukar hoto damar amfani da sadarwar ta VLAN wajen tura hotunnan da suka dauka kai tsaye ga editocinsu. Wannan shi ne karon farko da aka yi amfani da VLAN yayin wasannin Olympics domin aikewa da hotuna kai tsaye a lokacin da aka dauka.
Yayin wasannin Olympics na lokacin hunturu na 2022, da aka gudanar tsakanin ranar 2 zuwa 20 ga watan Fabrairu, a matsayinta na mambar tawagar masu daukar hotunan Olympics na kungiyar masu daukar hotuna ta kasar Sin, a karon farko, Zhao ta wakilci Jaridar yada labarai ta hotuna ta kasar Sin, wajen daukar hotunan wasannin Olympics.
Zhao ta ce, “akwai masu daukar hotunan yada labarai 735 da aka yi wa rejista domin wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing, daga cikinsu kuma, 140 Sinawa ne. Kuma ina alfaharin kasancewa daya daga cikinsu.”
A daren ranar 14 ga watan Fabrairun, yanayin sanyi ya kai maki 20 kasa da sifiri, a yankin dusar kankara na Genting, a birnin Zhangjiakou dake lardin Hebei na arewacin kasar Sin. Xu Mengtao mai shekaru 31 ta fafata a gasar wasan kankara ta Aerial Freestyle.
Tsallen Xu na karshe ya yi kyau sosai. Kuma ita ta lashe lambar zinare ta farko ga kasar Sin a irin wannan gasa ta Aerial Freestyle. “A karshe na yi nasara! Na yi nasara!” Cewar Xu cikin daga murya. Zhao Yingxin ta dauki hoton wannan lokaci na murna. Ta tsaya da kyamararta cikin dusar kankara sama da tsawon sa’o’i 4 yayin gasar. Zhao ta je yankin na Genting yayin wasannin har sau 5 domin daukar hotunan ‘yan wasa.
Beijing ya zama birni na farko da ya karbi bakuncin wasannin Olympics na lokacin zafi da na hunturu a tarihi. Yayin bikin rufe wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing, idanun Zhao sun cika da hawaye a lokacin da ta ji taken wasan Olympics na Beijing na 2008, mai suna You and Me, wato Ni da kai, yayin da zobban tambarin Olympics suka daga sama. Wannan ya tuna mata da shekarar 2008.
Yayin hirarraki sama da 30 a lokacin wasannin, Zhao ta dauki dimbin hotunan ‘yan wasan kasar Sin da suka lashe lambobin yabo dake kokarin cimma burikansu a wasannin Olympics, inda ta dauki hotunan da suka nuna kauna da goyon bayan dake tsakanin ‘yan wasa daga dukkan kasashe yayin da ake fuskantar annoba a duniya. Ta kuma dauki hotunan ma’aikatan sa kai da masu aikin kandagarki da takaita yaduwar annoba dake nuna yadda suke cike da kauna da kulawa. Hotunanta sun dauki yanayi mai aminci da kayatarwa na wasannin Olympics, haka kuma suna kunshe da ruhin wasannin Olympics na Beijing.(Kande Gao)