Ga yadda birnin Khartoum yake sakamakon rikicin dake tsakanin rundunonin soja na kasar
2023-05-15 08:42:35 CMG Hausa
Ya zuwa ranar 11 ga watan Mayu, rundunonin soja na kasar Sudan wadanda suke adawa da juna suna yakar juna a Khartoum, babban birnin kasar. Rikicin da aka shafe kusan wata guda ana gwabzawa a Sudan, ya sa birnin Khartoum ya zama wani fagen daga. Yanzu haka a kowace rana, mazauna birnin su kimanin miliyan 5 na shan wahalhalu iri iri da yakin ke haifar musu. (Sanusi Chen)