logo

HAUSA

Barawo ne ke yin ihun kama barawo

2023-05-15 14:28:17 CMG Hausa

Sakatariyar harkokin kudi ta kasar Amurka Janet Yellen ta halarci taron ministocin kudi da shugabannin manyan bankuna na kasashen kungiyar G7 a kwanan baya, inda ta yi kira da a dauki “matakai na bai daya”, don tinkarar abin da take kira wai “matakan tattalin arziki da kasar Sin ta dauka don tilasta wasu”. Lallai barawo ne ke yin ihun kama barawo ke nan, sakamakon yadda hakikanin al’amuran da suka faru suka shaida ainihin wadda ke daukar irin wadannan matakai.

In an tabo maganar “tilastawa” a huldar kasa da kasa, to za a gano cewa, Amurka da kanta ce ta kirkiro wannan ra’ayi tare da aiwatar da shi a kullum. In ba a manta ba, a shekarar 1971, Alexander George, shehun malami a jami’ar Stanford ya gabatar da ra’ayin nan na “matakan diplomasiyya don tilasta wasu”, don yin bayani a kan manufar kasar Amurka a kan kasashen Laos da Cuba da kuma Vietnam. Kasar Sin a nata bangaren, har kullum tana sa kaimi ga kasa da kasa da su bude kofarsu ta fannin tattalin arziki, kuma tana tsayawa tsayin daka a kan kin yarda da daukar matakan tattalin arziki don tilasta wasu.

A ganin kasar Amurka, moriya ce kawai za ta dore a maimakon zumunta. Don haka ma, ko kawayenta ma ba su tsira daga matakanta na tilas ba. In mun duba tarihi, kamfanin Toshiba na Japan da Siemens na Jamus da kuma Alstom na Faransa, wadanda dukkaninsu kamfanoni ne na kasashe kawayen kasar Amurka, duk sun fuskanci irin matakan da Amurka ta dauka, sakamakon yadda suka zama kalubale gare ta.  

Nan ba da jimawa ba, za a fara taron kolin G7, kuma da yawa daga cikin kasashen rukunin sun taba yin hasara sakamakon matakan tattalin arziki da Amurka ta dauka don tilasta su, wadanda ya kamata su yi tunani sosai a kan abin da ya faru gare su, idan dai Amurka ta kare aniyarta ta sanya batun “tinkarar matakan tattalin arziki don tilasta wasu” cikin ajandar taron.(Lubabatu)