logo

HAUSA

Amurka Ta Kau Da Kai Daga Yara ‘Yan Kwadago Cikin Shekaru Sama Da 200

2023-05-11 21:35:26 CMG Hausa

Yayin da a yanzu haka kasashen duniya suke sukar sanya yara shiga ayyukan kwadago, wannan yanayi ya zama ruwan dare a kasar Amurka.

Bisa kididdigar da ma’aikatar ‘yan kwadagon Amurka ta fitar, an ce, a shekarar 2022, miliyoyin yara suna aiki a fannonin aikin gona, da hidimomin sarrafa da sayar da abinci, da na sayar da kaya, da sha’anin nishadantarwa, da gine-gine, wadanda yawancinsu suka zo Amurka daga sauran kasashe. Kamfanin dillancin labaru na Reuters ya ruwaito cewa, tun bayan shekarar 2018, yawan yara ‘yan kwadago da aka yi hayarsu ba bisa doka ba a Amurka ya karu da kusan kaso 80%.

Amurka tana aiwatar da dokoki masu nasaba da yara ‘yan kwadago, wadanda aka fitar da su yau shekaru dari 1 da suka wuce, sakamakon ci gaban zamantakewar al’ummar kasar. Bisa dokokin kasar, ba a hana yara yin aiki, sai dai kawai akwai ka’idoji kan hakan. Don haka ake hayar yara su yi aiki a wasu sana’o’i bisa dokokin.

Ban da haka kuma, Amurka ta hana yara ‘yan kasa da shekaru 14 su yi aiki a yawancin sana’o’i, amma ban da aikin gona. Alkaluman cibiyar kula da lafiyar ma’aikatan da ke aiki a gandayen noma na Amurka masu zaman kan su sun nuna cewa, yara dubu 300 zuwa dubu 800, suna aiki a gandayen noma, ciki had da ‘yan kasa da shekaru 10.

Ya zuwa yanzu, Amurka ita ce kasa daya kacal cikin kasashe mambobin MDD guda 193, da ba ta sa hannu kan yarjejeniyar kiyaye hakkokin yara ba.

‘Yan siyasar Amurka suna amfani da kayayyakin da kananan yara suka samar, tare da sa baki kan hakkin dan Adam na wasu kasashe. Lallai Amurka ta kau da kai da nuna fuska biyu, da munafunci kan hakkin dan Adam.   (Tasallah Yuan)