logo

HAUSA

Tushen Huldar Sin Da Amurka Shi Ne Moriya Da Nauyi Na Bai Daya Dake Wuyansu Da Zumuncin Jama’arsu

2023-05-11 12:49:18 CMG HAUSA

DAGA MINA

Abokai, kawanan baya, jagoran jam’iyya mafi yawan mambobi a majalisar dattawan Amurka, kana dan jam’iyyar demokuradiyya Charles Ellis Schumer da sauran mambobin majalisar sun sanar da wani daftarin shirin doka mai suna “Yin takara da Sin 2.0”, da nufin cimma nasarar takara da kasar take yi da kasar Sin, ta hanyar kayyade zuba jari da fitar fasahohi gare ta. Ban da wannan shiri, majalisar dokokin kasar Amurka ta gabatar da shirye shirye da dama dake shafar kananan na’urorin lantarki da hada-hadar kudi da matsayin kasa mai tasowa da tsaro da sayar da makamai ga yankin Taiwan da sauransu, a yunkurin dakile ci gaban kasar Sin. Wadannan ‘yan siyasa cike suke da tunanin yakin cacar baka a kwakwalwansu, amma munanan matakan da suka dauka zai jefa huldar kasashen biyu cikin mawuyancin hali, kuma ita kanta ma za ta yi asara.

Mamba mai nazari na asusuan Carnegie na Amurka Jon Bateman ya wallafa wani sharhi a shafin yanar gizo na kafar yada labarai ta Politico, inda yake cewa, ‘yan siyasa dake matukar son yaki da kasar Sin, za su yi asara. A ganinsa, duk wani matakin da suke dauka na sanyawa kasar Sin shinge, ba shakka zai bata huldar kasashen, lamarin da zai kawo asara ga dukkan bangarorin. Dole ne, wadannan ‘yan siyasa su saurari shawara mai nagarta da aka bayar, sabo da tushen huldar kasashen biyu shi ne moriya da nauyi na bai daya dake wuyansu da ma zumuncin jama’ar kasashen biyu.(Mai zana da rubuta: MINA)