Sin ta yi nasarar harba kumbon dakon kaya samfurin Tianzhou-6
2023-05-11 21:26:39 CMG Hausa
An harba rokar Long March-7 Y7 dauke da kumbon dakon kaya samfurin Tianzhou-6 a yammacin jiya Laraba 10 ga watan nan daga filin harba taurarin dan Adam dake Wenchang na lardin Hainan na kasar, kuma bayan mintuna goma, kumbon ya rabu da rokar, ya kuma shiga falakin da aka tsara.