‘Yan wasan motsa jiki na Olympics sun nuna basirar su a fannin zane-zane
2023-05-11 16:41:04 CMG HAUSA
A baya bayan nan, wasu ‘yan wasan motsa jiki da suka halarci gasar Olympics ta duniya, sun baje fasahar su ta zane-zane, wadda ke nuna cewa suna da wasu hikimomi na daban baya ga fannin wasanni.
A ranar 23 ga watan Afirilun da ya shude ne kwamitin shirya gasar Olympic na kasa da kasa ko IOC, ya baje irin wadannan zane zane masu ban sha’awa guda 18, wadanda ‘yan wasa 5 da suka halarci gasar Olympic, da ajin gasar ta masu bukatar musamman ko Paralympics suka gabatar, wanda hakan ke nuna sassa daban daban na zane zanen su, mai kayatarwa, da kima ta manyan ‘yan wasan motsa jiki na duniya.
Sashen lura da al’adu da abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni na kwamitin IOC ne ya shirya baje irin wadannan zane zane, a karon farko a birnin Pyeongchang na koriya ta kudu a shekarar 2018, inda sashen ke ci gana da karbar zane zane wadanda a yanzu yawan su ya haura 50, daga ‘yan wasan motsa jiki 16, da suka fito daga kasashe da yankuna 8, kuma har yanzu sashen na kara karbar wasu.
Da take tsokaci game da hakan, Manajar Asusun raya shirye shiryen al’adu, da abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni na kasa da kasa Anja Wodsak, ta ce "Mun lura da cewa akwai ‘yan wasan Olympics da dama da suke da basirar zane zane, kuma hakan ya ba da sha’awa kwarai, musamman duba da yadda daidaikun su ke da sha’awa a wannan fanni, wadanda ke da basira baya ga harkar wasa".
Wodsak ta kara da cewa, "Ko wane daya cikin wadannan ‘yan wasan Olympic ya shata layi, tsakanin yadda yake kallon harkar zane zane da kuma fannin wasannin motsa jiki a rayuwa. Ga mafi yawan su, zane zane bangare ne mai samar da gamsuwa a rai. Kuma ya yi kama da sauran ayyukan da suke kama da na yau da kullum, wato yadda mutum ya so yake yin su. Wasu kuwa na ganin zane zanen na samar da daidaito tsakanin sana’a da sauran bangarorin rayuwa. Idan mutum ya je wuraren da ake baje kolin zane zane yana samun natsuwa, suna da ban sha’awa. Saboda hanya ce ta daidaita yanayin jiki da na zuciya".
Kaza lika, sashen lura da al’adu da abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni na kwamitin IOC ya jagorancin shirye shirye 2, daya a birnin Tokyo a shekarar 2020 da kuma a birnin Beijing a shekarar 2022, kana sashen ya jagoranci shirin watanni 3, na zabar wadanda za su gabatar da karin zane zane cikin ‘yan wasan na motsa jiki, domin gasar birnin Paris a shekarar 2024. Tuni kuma ‘yan wasan Olympics 82, da na ajin Paralympic 11 daga kasashe da yankuna daban daban har 32 sun yi rajista.
Mai zane zanen fenti, kuma dan wasan linkaya Gregory Burns daga Amurka, ya shiga gasar Paralympic har sau 3. Kuma yayin zantawar sa da sashen na raya al’adu na IOC, Burns ya ce dukkanin su ‘yan wasa na bukatar yanayin tunani da na jiki mai karfi, da kuma atisayen ruhi. Dukkanin su suna da son abubuwa masu ban sha’awa da kayatarwa, don haka wannan aiki ne mai faranta rai irin wanda ‘yan wasan ba su cika gani ba.
Shi ma dan wasan kwallon kafa daga kasar New Zealand Hannah Wilkinson, wanda ya wakilci kasar sa a gasar Olympic har sau 3, ya ce "Manyan ’yan wasan motsa jiki wani lokacin suna fuskantar matsi mai wahalarwa. Idan an shiga irin wannan yanayi, samun damar yin zane zane yana nishadantar da mu, da ba mu daidaito."
Kari kan abubuwan da ta fada, Wodsak ta nazarci zane zane da ‘yar wasan zamiyar kankara daga kasar Canada Laurenne Ross ta gabatar, inda ta ce wasu lokutan ‘yan wasan motsa jiki na shiga matsi na fatan lashe gasanni. Don haka ya kamata su rika tunawa kan su cewa, suna yin wannan wasanni ne domin suna ba su sha’awa, kuma zane zanen hanya ce ta bayyana abun da ke cikin zukatan su".
Wodsak ta kara da cewa, Ross wadda ta shiga gasar Olympics a Sochi a shekarar 2014, da gasar birnin PyeongChang a shekarar 2018, a yanzu tana daf da kammala karatun digiri a fannin zane zanen gine gine. A shekarar 2022, Ross ta fitar da wani karamin faifan bidiyo game da yadda ta gudanar da zaman ta a birnin Beijing a shekarar 2022, kasancewar ta ‘yar wasan motsa jiki kuma mai zane zane.
A nasu bangaren kuwa, dan wasan tsere da tsallake shinge daga Slovakia Slaven Dizdarevic, da dan wasan jifan javelin daga Birtaniya Roald Bradstock, suna gudanar da sana’ar su ta tsere da kuma zane zanen fenti, yayin da Kelly Salchow MacArthur daga Amurka ita ma ke daidata rayuwarta, ta wasan tseren kwale-kwale da kuma zane zane.
“Yan wasan motsa jiki da dama dai na zabar fannonin nuna fasahohi daban daban, kama daga zane zane fenti zuwa zanen fensir, da kade kade da sassaka, da daukar hoto, da zane mai hade da rubutu da hotuna, da kayata wurare, da nuna fasahohin wasan kwaikwayo, da fannin rubutun labarai da shirya fina-finai –wadanda dukkanin su ke ba da damar bayyana basirar bil adama.
Game da hakan Wodsak ta ce "Daya daga muhimman dalilan da suke sa mu yi zabe, shi ne muna bukatar nuna yarukan basira daban daban, kuma hakan na baiwa ‘yan wasan Olympics damar shakatawa. Suna shiga a dama da su. Suna kawo mana sakamakon, fiye da yadda muke zaton za su iya".
Ana iya ganin ayyukan zane zane na ‘yan wasan Olympics kan yanar gizo, kamar yadda aka baje kolin su yayin gasannin Olympics na birnin Beijing a shekarar 2022, da na Tokyo na shekarar 2020. Kaza lika za a gudanar da baje kolin ayyukan a daukacin kwanakin watan Disambar shekarar nan ta 2023.
……………………………………………………………………………………………………………………………………………………..Feature: Olympian artists create world beyond sports