logo

HAUSA

Ousmane Boubey Oumarou: Zan bada tawa gudummawa wajen kara samun fahimtar juna tsakanin al’ummomin Nijar da China

2023-05-09 16:00:21 CMG Hausa

Kwanan baya, wato a ranar 18 ga watan Afrilun bana, an kaddamar da kasaitaccen bikin matasan Sin da Afirka karo na 7 a Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Shirya bikin ya samo asali ne tun daga taron kolin dandalin tattauna hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a takaice, wanda aka gudanar a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a shekara ta 2015, wanda ya zama ra’ayin bai daya da aka cimma tsakanin shugabannin Sin da Afirka, da nufin inganta mu’amala tsakanin matasan bangarorin biyu, da kara sada zumunta tsakanin su. Tun shekara ta 2016, ya zuwa yanzu, an riga an shirya irin wannan biki har sau shida.

Bikin na bana, an gudanar da shi ne a muhimman wurare biyu a kasar Sin, ciki har da birnin Beijing, da lardin Shandong, inda wakilan matasan Afirka suka ziyarci birane da yankunan karkara, don ganema idanun su ci gaban kasar a fannoni daban-daban.

Daga cikin mahalarta bikin, akwai wani dan asalin Jamhuriyar Nijar, mai suna Ousmane Boubey Oumarou. A zantawar sa da Murtala Zhang, malam Ousmane ya ce wannan shi ne karon farko da ya zo China, kuma kamar yadda akan ce “Gani ya kori ji”, irin ci gaban kasar gami da al’adun gargajiyar ta sun burge shi kwarai da gaske.

Malam Ousmane ya kuma bayyana kyakkyawan fatan sa ga ingantar hadin-gwiwa, da karfafar zumunta tsakanin Nijar da China. (Murtala Zhang)