logo

HAUSA

Wani babban dalilin da ya haifar da hargitsi a kasar Sudan

2023-05-09 16:21:32 CMG Hausa

Sanin kowa ne, kasar Amurka tana kallon kanta a matsayin “mai kare tsarin Demokuradiyya” a duniya. Sai dai yunkurin kasar na “kare Demokuradiyya” ya kan haddasa ta’asa a sauran kasashe.

Kwanan baya, na karanta wani bayanin da shafin yanar gizo na jaridar New York Times ta kasar Amurka ya watsa, mai taken “ Yadda yunkurin kasar Amurka na tabbatar da tsarin Demokuradiyya a Sudan ya haddasa yaki a kasar”. Marubucin wannan bayani ya ce, kasar Amurka ta dade tana kokarin mai da kasar Sudan wani misali na gwajin yada tsarin Demokuradiyya a sauran kasashe, inda ta yi ta shisshigi cikin harkokin siyasa na kasar. Sai dai kamar yadda ake cewa “Domin auki ake yin kunu ya komo ya rasa auki”, goyon bayan da kasar Amurka ta nuna wa manyan hafsoshin kasar Sudan ya sa su girman kai da kwadayin ikon mulki, lamarin da ya sa ake samun barkewar wutar yaki a kasar yanzu.

Wannan bayani ya nuna yadda kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka yi tsokaci game da manufar kasar ta “yada tsarin Demokuradiyya” a duniya. Ra’ayin marubucin bayanin na “manufar kasar Amurka ta haddasa hargitsi a kasar Sudan” ya yi daidai, amma bai fayyace ainihin dalilin da ya sa ake samun wannan sakamako ba. A ganinsa, idan kasar Amurka ta saka wa shugabannin sojojin kasar Sudan takunkumi a maimakon nuna musu goyon baya, to, za a iya tabbatar da tsarin Demokuradiyya a kasar. Sai dai, a hakika, yadda kasar Amurka take shisshigi a harkokin kasar Sudan, da fakewa da batun Demokuradiyya, shi ne babban dalilin da ya sa ake ta samun rikice-rikice a kasar.

Tun da tsohon shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya kama mulki a shekarar 1989, kasar Amurka ta fara kokarin neman kawo karshen mulkinsa. Daga farkon shekarun 1990, kasar Amurka ta hure wa gamayyar kasa da kasa kunne, don su dakatar da samar da tallafi da rance ga kasar Sudan, bisa dalilin wai kasar na “keta hakkin dan Adam”.

Daga baya, kasar Amurka ta kara sanya wa kasar Sudan takunkumi, bisa zarginta da “nuna goyon baya ga ‘yan ta’adda”. Matakan da kasar Amurka ta dauka sun sa Sudan zama wata kasa dake “rike da kwanon zinariya tana barace-barace”, ganin yadda kasar ta kasa raya tattalin arzikinta, inda ta kai har kashi 47% na al’ummar kasar sun tsunduma cikin tsananin talauci, duk da kasar na mallakar dimbin albarkatun kasa, ciki har da danyen mai.

Ban da matakan tattalin arziki, kasar Amurka ta kuma dauki matakai na siyasa, don neman hambarar da shugaba al-Bashir. Inda ta dade tana samar da tallafi ga dakaru masu adawa da gwamnatin Sudan, ciki har da dakarun yankin Darfur, da na yankin da aka fi samun danyen mai dake kudancin kasar. Lamarin da ya sa ake ta samun tashin hankali a kasar Sudan, da yukurin ballewar yankin kudancin kasar, wanda ya zama kasar Sudan ta Kudu daga bisani.

Wannan lamari ya sa kasar Sudan asarar kashi 70% na albarkatun mai, da fuskantar raguwar kudin shiga, da tsanantar yanayin koma bayan tattalin arziki, abun da ya sa dimbin jama’ar kasar aiwatar da zanga-zanga a wurare daban daban sakamakon matukar fushi. Daga baya, bisa goyon bayan da kasar Amurka ta bayar, Abdel Fattah al-Burhan, da sauran manyan hafsoshin rundunar sojan kasar suka kaddamar da juyin juya hali, wanda ya kai ga hambarar da shugaba Omar al-Bashir a shekarar 2019.

Kasar Amurka ta kwashe shekaru 30 tana kokarin neman kawo karshen mulkin Omar al-Bashir, kuma a karshe ta samu biyan bukata. Sai dai hakan bai sa kasar Sudan karkata ga turbar Demokuradiyya ba. Maimakon haka, an dade ana samun ja-in-ja tsakanin rukunonin sojan kasar. Har ma wannan yanayi ya sa an sa kafar wando daya, tare da juyewa zuwa wani babban tashin hankali mai tsanani yanzu. Sai dai sau da yawa mun ga abkuwar makamancin hakan, inda kasar Amurka ta yi shisshigi cikin harkokin gidan sauran kasashe, har ma ta hambarar da gwamnatocin kasashen, ta fakewa da “kare Demokuradiyya”, daga baya kuma kasashen suka fada cikin tarkon tashin hankali, da tabarbarewar tattalin arziki. Kuma da wuya su iya fitar da kansu daga cikin irin wannan tarko. Wannan lamari ya taba faruwa a kasashen Iraki, da Afghanistan, da kuma Libya.

Bayanin jaridar New York Times ya nuna cewa, ko Amurkawa ma ba su gamsu da matakan gwamnatin kasarsu na yada tsarin Demokuradiyya ba. A ganinsu, watakila za a iya daidaita aikin, ta hanyar kyautata dabarun shisshigi, misali nuna goyon baya, ko kuma sanya takunkumi kan sauran mutane.

Duk da haka, a matsayin mu na mutane na sauran kasashe, abin da muke son fada shi ne: Lokaci ya yi a kawo karshen girman kai na kasar Amurka. Idan kasar za ta iya girmama ikon mulkin kai na sauran kasashe, da daina yin shisshigi cikin harkokin gidansu, to, hakan zai iya zama gudunmowa mafi girma da kasar Amurka za a iya samar wa duniya, a fannin kare darajar Demokuradiyya. (Bello Wang)