logo

HAUSA

Yadda ake kare tsoffin gine-gine a kasar Sin

2023-05-08 09:28:11 CMG Hausa

Rana 18 ga watan Afrilu, rana ce ta kare tsoffin gine-gine masu darajar tarihi ta kasa da kasa. A wannan rana ta musamman ta bana, wasu hukumomi na birnin Beijing sun gudanar da wani taro, inda wasu jami'an gwamnati da kwararru suka tattauna manufofi, da dabarun da kasar take dauka, don kare tsoffin gine-gine a wani sabon zamani da muke ciki, gami da wasu abubuwan da ya kamata a ci gaba da lura da su a nan gaba. (Bello Wang)