logo

HAUSA

Masu fama da ciwon kansa a kasashe masu yawan kudin shiga sun fi samun damar tsira daga mutuwa

2023-05-07 15:18:51 CMG Hausa

 

Wata kungiyar nazari ta duniya ta kaddamar da rahotonta a baya-bayan nan cewa, masu fama da ciwon kansa da suke zama a kasashe 7 masu yawan kudin shiga, ciki had da kasar New Zealand, sun samu karuwar damar tsira daga mutuwa cikin kusan shekaru 20 da suka gabata, amma akwai bambamci a tsakanin kasahen.

Kungiyar nazarin da ke karkashin shugabancin hukumar kula da ciwon kansa ta kasar New Zealand ta kaddamar da rahoton nazarin ne cikin shahararriyar mujallar lafiya ta Lancet ta kasar Birtaniya a kwanan baya, inda ta yi bayani da cewa, manazarta sun tantance yawan masu fama da nau’o’in ciwon kansa iri iri guda 7 wadanda suka tsira daga mutuwa, suka ci gaba da rayuwa bayan da aka yi musu jinya, a kasashen New Zealand, Australiya, Canada, Denmark, Ireland, Norway da Birtaniya daga shekarar 1995 zuwa ta 2014. Wadannan cututtukan kansa 7 sun hada da nau’in ciwonkansa na makogwaro, tumbi, uwar hanji da sauran wasu nau’o’i kansa 4, da a kan yi fama da su.

Sakamakon nazarin ya nuna cewa, a cikin shekaruu kusan 20 da suka gabata, a cikin wadannan kasashe 7 masu yawan kudin shiga, yawan masu fama da ciwon kansa iri iri guda 7 da muka ambato a baya, da suka tsira daga mutuwa sun ci gaba da rayuwa cikin shekara 1, da kuma shekaru 5 bayan da aka yi musu jinya, sun dan karu. Amma akwai bambanci a tsakanin wadannan kasashe 7 masu yawan kudin shiga. Alal misali, daga shekarar 2010 zuwa ta 2014 ne yawan masu fama da ciwon kansa da suka tsira daga mutuwa bayan da aka yi musu jinya a kasashen Australiya, Canada da Norway, ya fi na wadanda suke zama a kasashen New Zealand, Denmark, Ireland, da Birtaniya.

Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, binciken da aka yi kan yawan masu fama da ciwon kansa wadanda suka tsira daga mutuwa bayan da aka yi musu jinya, ya amfana wajen ba da hidima mai dacewa kan masu fama da ciwon kansa, tare da yin hasashe kan yiwuwar tsira daga mutuwa sakamakon kamuwa da cutar.