Bikin Canton Fair ya samar da dimbin damammakin kasuwanci
2023-05-06 18:13:19 CRI
[!--begin:htmlVideoCode--]3a3f353536e34d90b0a0b420d3b50a5d,0,1,,news[!--end:htmlVideoCode--]
A ranar 5 ga wata, an kawo karshen bikin kasuwanci na Canton Fair karo na 133, da ake gudanarwa a birnin Guangzhou na kasar Sin. Yadda aka karya bajintar tarihi a fannonin fadin wurin gudanar da bikin, da yawan kamfanonin kasashe daban daban da suka halarta, ya nuna tasirin bikin Canton Fair, da karfinsa a fannin jan hankalin ‘yan kasuwan sassan duniya.