logo

HAUSA

Yadda hukumar CIA ta Amurka ke aikata mugunta wajen satar bayanan sirri

2023-05-06 16:00:06 CMG Hausa

“Muna karya. Muna yaudara. Muna sata.” Irin wadannan kalaman da ‘yan siyasar kasar Amurka suka yi kan hukumar leken asirin kasar wato CIA, na dada yaduwa tsakanin al’umma. A hakikanin gaskiya, yayin da harkokin yanar gizo ta intanet ke kara bunkasa, ya dace a kara wasu kalmomi, wato “muna leken asiri, muna kai hari, muna rura wutar rikici”.

Kwanan nan, cibiyar kar ta kwana ta yaki da harin Virus na na’urori masu kwakwalwa ta kasar Sin, da hadin-gwiwar kamfanin 360 mai kula da tsaron yanar gizo na kasar, sun fitar da wani rahoton bincike, inda aka fayyace yadda CIA din ta dade tana tattaro bayanan sirri da suka shafi gwamnatoci, da kamfanoni gami da daidaikun al’umma na kasashe daban-daban, da gudanar da ayyukan leken asiri a sassa daban-daban a duniya.

Alkaluman sun shaida cewa, a shekaru sama da goma, CIA ta riga ta kifar ko kuma ta yi yunkurin kifar da wasu halastattun gwamnatoci akalla 50, tare da hura wutar rikici a kasashe da dama.

Hakan ya sa jama’a suka kara fahimta cewa, gaskiya Amurka ta cancanci wannan lakabin da aka yi mata, wato “kasar dake da gungun kwararrun masu aiwatar da harin yanar gizo”, kana, hukumar CIA  tana nan tana ci gaba da haifar da barazana ga tsaro gami da ci gaban duk duniya. (Murtala Zhang)