logo

HAUSA

Mummunan aiki na kai hari ga sauran kasashe ta yanar gizo

2023-05-05 15:27:54 CMG HAUSA

A cikin shirin yau bari mu mai da hankali kan wani rohoton da aka gabatar dangane da munanan ayyukan da hukumar CIA ta kasar Amurka ta yi na kai hari ga sauran kasashe ta yanar gizo:

 

Cibiyar kar ta kwana ta yaki da harin Virus na na'urori masu kwakwalwa ta kasar Sin, da hadin gwiwar kamfanin 360 mai kula da tsaron yanar gizo na kasar, sun fitar da wani rahoton bincike mai taken “hukumar leken asirin Amurka ta CIA ta kasance gungun kwararrun masu aiwatar da harin yanar gizo”a jiya Alhamis 4 ga wata.

 Rahoton ya yi bayani game da batun kai hari kan sauran kasashe da hukumar CIA ta yi ta yanar gizo, ya kuma ba da misalin wasu hare-haren da aka kai kasar Sin da wasu kasashe daban daban, ta yanar gizo, tare da nazari kan ayyukan leken asiri na hukumar CIA, da gudummawar da ta bayar ga kasar Amurka na kasancewa kasar dake kokarin leken asiri ta yanar gizo a duniya. Rahoton zai zama abin misali da shawara ga masu gamuwa da harin yanar gizo daga sassan duniya.