logo

HAUSA

Sin ta shirya samar da hidimomin tafiye-tafiye yayin bikin ma’aikata na kasa da kasa

2023-05-05 15:26:56 CRI

 Masu kallo, gabannin bikin ma’aikata na kasa da kasa, fasinjoji masu yawon bude ido sun yi matukar karuwa a bayyane, ana ta ganin yawaitar matafiya masu bin jiragen kasa, da hanyoyin mota, da filayen jiragen sama, da kuma tashoshin ruwa, don haka hukumomin da abin ya shafa suka riga suka shirya sosai, domin samar da hidimomi gare su:

A kwanan baya, majalisar gudanarwar kasar Sin, ta sanar da cewa, tsayin hutun bikin na bana zai kai kwanaki biyar, wato tun daga ranar 29 ga watan Afililun nan har zuwa ranar 3 ga watan Mayu dake tafe.

Kaza lika a jiya Alhamis, hukumar shige da fice ta kasar Sin ta bayyana cewa, matsakaicin adadin mutanen da za su shiga kasar ko fita zuwa ketare, zai kai mutum miliyan 1.2 a ko wace rana yayin bikin na bana, adadin da zai karu da ninki daya, kan na makamancin lokaci na bara.

Ban da haka, matsakaicin adadin motocin da za su bi hanyoyi zai kai tsakanin miliyan 533 zuwa miliyan 543 a ko wace rana a fadin kasar, adadin da zai karu da kaso 73 bisa dari, zuwa kaso 77 bisa dari.