logo

HAUSA

Karuwar yawon shakatawa ta nuna yanayi mai kyau na tattalin arzikin Sin

2023-05-05 11:23:32 CMG Hausa

Alkaluman da wasu hukumomin kasar Sin suka gabatar sun nuna cewa, tsakanin ranar 29 ga watan Afrilun da ya gabata, da ranar 3 ga watan Mayun da muke ciki, wato lokacin da Sinawa suke hutun ranar ma’aikata, yawan mutanen da suka yi zirga-zirga don yawon bude ido a kasar Sin ya kai miliyan 274, jimillar da ta karu da kashi 70.83% bisa ta makamancin lokacin bara. Kana kudin da aka samu cikin wannan gajeren lokaci, a fannin yawon shakatawa, ya kai kudin Sin Yuan biliyan 148.06, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 21.4, adadin da ya karu da kashi 128.90% bisa na makamancin lokacin bara.

A bana, kasar Sin ta dora muhimmanci kan aikin farfado da habaka harkar sayayya, inda ta gabatar da jerin matakai na ba jama’a damar samun karin kudin shiga, da kyautata muhallin sayayya, da dai sauransu. Daga baya tattalin arzikin kasar ya samu karuwar da ta wuce yadda aka zata, a cikin watanni 3 na farko na bana, haka kuma alkaluman da aka samu a lokacin hutun ranar ma’aikata su ma sun zarce yadda aka yi hasashe a baya. Wadannan abubuwa sun nuna cewa, an samu farfadowa sosai a bangaren sayen kayayyaki a kasar Sin, kana karuwar sayayya na samar da karin gudunmowa ga farfadowar tattalin arzikin kasar.

A sa’i daya kuma, karuwar bukatun da ake samu a cikin gidan kasar Sin ita ma ta taimaki tattalin arzikin duniya wajen samun farfadowa. Wani rahoton da hukumar ba da lamuni ta duniya IMF ta gabatar a kwanan nan ya nuna cewa, kasar Sin tana kan gaba a cikin dukkan kasashen dake yankin Asiya da na tekun Pacific, wajen samar da gudunmowa ga karuwar tattalin arzikin duniya.

Ban da haka, manufar kasar Sin ta neman samun ci gaba mai inganci ta sa ake samun karin bukatu a kasuwannin kasar, kan abubuwan da suka hada da motoci masu amfani da sabbin makamashi, da gidaje masu inganci, da dai sauransu, lamarin da ke samar da dimbin damammaki na samun ci gaban tattalin arziki ga kasashe daban daban. (Bello Wang)