logo

HAUSA

Matasa masu aikin harhada rokoki masu dakon kaya

2023-05-04 20:15:47 CMG Hausa

Malam Luo Xinsheng ke nan, wanda aka haife shi a shekarar 1988, wanda kuma yake aiki a kamfanin nazarin kimiyyar sararin samaniya na kasar Sin. Luo Xinsheng tare da abokanan aikinsa ne suke daukar nauyin harhada sabbin salon rokoki masu dakon kaya. A hakika, a wajen aikin harhada rokokin, ana yawan samun matasa irin Luo Xinsheng, wadanda matsakaicin shekarunsu ya kai 29, wadanda suka kammala jerin ayyuka na harhada rokoki. Kamar dai yadda Luo Xinsheng ya ce, “A gaba, matasa na zamaninmu ne za mu gudanar da aikin binciken sararin samaniya, kuma nauyin da ke wuyanmu ne mu yi kokarin cimma mafarkin.”