logo

HAUSA

Richard Sears:Harufan Sinanci ba kawai na kasar Sin ba ne, al’ada ce mai daraja ga duniya baki daya

2023-05-03 20:13:49 CRI

Ranar 20 ga watan Afrilun kowace shekara, rana ce ta harshen Sinanci da MDD ta tsai da. A halin yanzu da kasar Sin ke ta kara mu’amala da kasashen duniya, al’ummun kasashe daban daban ma na kara sha’awar koyon Sinanci, kuma Richard Sears, wani masani dan kasar Amurka na daya daga cikinsu.

Richard Sears yanzu haka yana zaune a birnin Nanjing, hedkwatar lardin Jiangsu na kasar Sin, kuma ya shafe shakaru da dama yana nazarin harufan Sinanci, har ma ya kafa wata ma’adanar bayanai na harufan Sinanci na ainihi. A ganinsa, harufan Sinanci ba kawai na kasar Sin ba ne, domin kuwa su wata al’ada ce mai daraja ga duniya baki daya.

A kasance tare da mu cikin shirin, don jin karin haske.(Lubabatu)