Aisar Tijjani Chinade: Ina kira ga matasan Najeriya da su zo kasar Sin don bude ido da samun ilimi
2023-05-02 15:29:56 CMG Hausa
Aisar Tijjani Chinade, dalibi ne dan asalin jihar Bauchin Najeriya, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na biyu a jami’ar koyon ilimin fasaha da kasuwanci ta Beijing, wato Beijing Technology and Business University.
A wata zantawar sa da Murtala Zhang, malam Aisar Tijjani Chinade, ya bayyana abubuwan da suka burge shi a kasar Sin, da ci gaban kasar a ra’ayin sa.
Har wa yau, ya jaddada muhimmiyar rawar da matasa suke takawa a harkokin yau da kullum, da yin kira ga mutanen Najeriya, musamman matasa, da su zo kasar Sin don bude ido da samun ilimi. (Murtala Zhang)