Lan Zhen, wadda ke dukufa wajen inganta aikin koyarwa na karkarar kasar Sin
2023-05-01 15:37:06 CMG Hausa
Lan Zhen, daraktan rashen Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin dake makarantar firamare ta Zhangzhou a birnin Zhangzhou na lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin, ta shaidawa manema labarai a baya-bayan nan cewa, tana alfahari da zaben da aka yi mata a matsayin wakiliyar taron mambobin JKS karo na 20 da aka yi a watan Oktoban bara. Cikin watannin da suka gabata, ta gabatar da jawabai a jami’o’in da kwalejoji da makarantun firamare da na midil dake yankin, domin yayata ruhin taron. Ta jadadda cewa ya kamata malamai su mayar da hankali wajen horar da masu gado ra’ayin gurguzu, wadanda suke da gogewa da ilimi da lafiya da basira da kwarewar aiki. Lan ta kuma karfafawa dukkan malamai da dalibai gwiwar shigar da ra’ayoyinsu cikin aikin farfado da kasar Sin. Ta kuma yi kira ga malamai su kara taka rawa wajen taimakawa yaran karkara samun ingantaccen ilimi.
An haifi Lan ne a kauyen kabilar She dake birnin Zhangzhou. A lokacin da take karama, Lan ta lura cewa, galibin mutanen kauyen na girmama mahaifiyarta, wadda malama ce a daya daga cikin makarantun firamare na kauyen, kafin ta yi ritaya. Daga wancan lokaci, Lan ta kuduri niyyar bin sahun mahaifiyarta.
A 1988, Lan ta fara koyar da harshen Sinanci a wata makarantar firamare dake karkashin kwalejin horar da malamai ta Longxi, wata gunduma a Zhangzhou. A 1990, a karon farko, Lan ta lashe lambar yabo ta gasar tsara ka’idojin koyar da Sinanci ta malaman firamare, wadda gidan talabijin na lardin ya shirya. Ita ce mafi kankantar shekaru cikin wadanda suka shiga gasar. Daga baya ba da dadewa ba kuma ta samu lambar yabo ta farko yayin gasar koyar da harshen Sinanci ta malaman firamare.
Zuciyar Lan ta cika da farin ciki yayin da ta shaida sauye-sauye a tsarin ilimin yankunan karkara. Sai dai ta fahimci cewa, ana bukatar karin kokari wajen inganta ilimi a yankunan karkara da dama dake kasar Sin. Tana ganin cewa, ya zama wajibi ta yi wani abu domin taimakawa yaran karkara samun ilimi mai inganci.
A shekarar 2013, Lan ta kafa wata cibiya a Zhangzhou, domin taimakawa malaman kauye wajen inganta dabarunsu na koyarwa. Ofishin kula da ilimi na Zhangzhou, ya ayyana wannan cibiya a matsayin wajen gwajin aiwatar da shirin horar da malaman karkara.
Cikin shekarun da suka gabata, malaman kauye da dama a Fujian, sun samu horo kan dabarun koyarwa karkashin wannan shiri. Mashirya shirin sun kuma shirya yadda masu karbar horon za su samu darrusa daga malamai daga makarantun firamare daban-daban dake Xiamen, wani birni a Fujian. Lan ta bayyama cewa, “darussan sun wayar da kan wanda ke karbar horon, domin sun taimaka musu wajen kara kokarin inganta dabarunsu na koyarwa.”
A 2017, ofishin kula da ilimi na Zhangzhou, ya ayyana makarantar firamare ta Zhangzhou a matsayin cibiya daya tilo ta horar da malaman kauye a birnin. A 2018, sashen kula da ilimi na lardin Fujian, ya yi wa cibiyar lakabi da “Fujian Lanzhen’s Famous Teachers’ Studio” wato cibiyar horar da malamai ta Lan Zhen ta Fujian.
Cikin shekaru 10 da suka gabata, mambobin cibiyar sun koyar da dalibai a yankunan karkara na yankuna daban-daban na lardin Fujian. Sun kuma horar da malaman makarantu da dama.
Kusan malaman karkara 900, wadanda suka samu horo a cibyar, sun zama jagorori a makarantunsu mabanbanta. Lan Zhen na fatan za a samu karin hazikan malamai karkashin shirin na horar da malaman kauye. Ta kuma yi fatan kungiyoyi daban-daban da mutane daga sassa daban daban na zamantakewar al’umma a fadin kasar, za su bayar da karin muhimmanci wajen inganta harkar ilimi a karkarar kasar Sin.
Cikin shekaru 30 da suka gabata, Lan ta sadaukar da lokacinta wajen yada basira ga yara da kara musu kwarin gwiwa. Yayin da take aiwatar da gyare-gyare kan salon koyarwa, ta gano abun da take son yi, wato inganta ilimi a yankunan karkarar kasar Sin.
Cikin shekaru da dama da suka gabata, Lan ta jagoranci mambobin cibiyarta wajen ziyartar makarantun firamare a yankuna da gundumomi daban-daban dake Zhangzhou, ta yadda za su iya gani da idanunsu, bukatun malaman makaranta, da kuma wahalhalun da suke fuskanta, yayin da suke koyarwa.
Tun bayan da aka zabe ta matsayin wakiliyar taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin na NPC karo na 11 a shekarar 2008, Lan ta gabatar da gomman shawarwari domin inganta raya tsarin ilimin kasar Sin. Misali, ta yi kira da a kara kokarin tilasta samun ilimi a fadin kasar, da karfafa ilmantar da iyalai, ta yadda yara za su tashi cikin aminci. Lan ta gabatar da shawarwari da dama na inganta ilimi a yankunan karkara, ciki har da farfado da ilimi a yankunan karkara da samar da kwararrun malamai. A ganinta, kowacce shawara kamar yaro ne karami, inda ta jajirce sosai wajen ganin an aiwatar da ita.
Lan na farin ciki ganin ingantuwar da aka samu a tsarin ilimin karkarar kasar Sin. Ta ce, “Ya kamata mu yi iyakar kokarinmu na ganin mun zaburar da malaman kauye sun fara kaunar aikinsu. Kuma ya kamata mu shawo kan kalubalen da inganta tsarin ilimin yankunan karkara a kasar Sin ke fuskanta.”
Yayin da take koyar da yara a yankunan karkara daban-daban dake lardin Fujian, Lan ta gano cewa, duk da cewa yaran karkarar na samun littattafai da dama daga masu bayar da gudunmuwa, da yawa daga cikinsu ba su gane yadda ake karatu, kuma malamai kalilan ne ke iya taimaka musu yadda ya kamata yayin da suke karantun littattafan. Cikin shekaru da dama da suka gabata, Lan ta lalubo hanyoyin taimakawa malaman karkara inganta kwarewarsu na koyar da dalibansu, musammam bayan lokacin makaranta.
Lan ta kuma shirya tarukan karawa juna sani a yankunan karkara, domin yayata ilimi da bayanai game da manufofin kasa da na JKS. Ta ce, “tun da aka zabe ni matsayin wakiliyar taron NPC na 11, na zama kakakin malaman kauyuka. Bisa la’akari da bukatu da fatan malaman karkara, na gabatar da shawarwari kan yadda za a inganta ilimi a yankunan karkara yayin tarukan shekara shekara na NPC. Na kuma yi iyakar kokarina wajen taimakawa malaman kauyuka inganta kwarewarsu na koyar da dalibansu.” Haka kuma ta kara da cewa, “Ina fatan gwamnatin kasar Sin za ta kara daukar manufofin jan hankalin karin masu basira domin su bi sahun malaman karkara wajen samar da ilimi mai inganci ga yaran karkara.”
Lan da ta shafe shekaru 35 tana koyarwa, ta shaida manyan ci gaban ilimi na kasar Sin. A lokacin da aka zabe ta don halartar taron wakilan JKS karo na 20 a bara, Lan ta ce, “A matsayin malama, inganta ilimin kasa hakki ne da ya rataya a wuyana. Zan yi iyakar kokarin ganin yara sun cimma burikansu.”
Masu sauraro, da haka muka kawo karshen shirinmu na yau na In Ba Ku Ba Gida, da fatan kun ji dadinsa. A madadin Fa’iza Mustapha da ta fassara bayanin, ni Kande da na shirya muku shirin nake cewa a kasance lafiya daga birnin Beijing.(Kande Gao)